< Yohanna 19 >
1 Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.
Τότε οὖν ἔλαβεν ὁ Πιλᾶτος τὸν Ἰησοῦν καὶ ἐμαστίγωσεν.
2 Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya.
καὶ οἱ στρατιῶται πλέξαντες στέφανον ἐξ ἀκανθῶν ἐπέθηκαν αὐτοῦ τῇ κεφαλῇ, καὶ ἱμάτιον πορφυροῦν περιέβαλον αὐτόν,
3 Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
καὶ ⸂ἤρχοντο πρὸς αὐτὸν καὶ ἔλεγον· Χαῖρε, ὁ βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων· καὶ ἐδίδοσαν αὐτῷ ῥαπίσματα.
4 Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.”
⸂καὶ ἐξῆλθεν πάλιν ἔξω ὁ Πιλᾶτος καὶ λέγει αὐτοῖς· Ἴδε ἄγω ὑμῖν αὐτὸν ἔξω, ἵνα γνῶτε ὅτι ⸂οὐδεμίαν αἰτίαν εὑρίσκω ἐν αὐτῷ.
5 Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
ἐξῆλθεν οὖν ὁ Ἰησοῦς ἔξω, φορῶν τὸν ἀκάνθινον στέφανον καὶ τὸ πορφυροῦν ἱμάτιον. καὶ λέγει αὐτοῖς· ⸀Ἰδοὺὁ ἄνθρωπος.
6 Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
ὅτε οὖν εἶδον αὐτὸν οἱ ἀρχιερεῖς καὶ οἱ ὑπηρέται ἐκραύγασαν λέγοντες· Σταύρωσον ⸀σταύρωσον λέγει αὐτοῖς ὁ Πιλᾶτος· Λάβετε αὐτὸν ὑμεῖς καὶ σταυρώσατε, ἐγὼ γὰρ οὐχ εὑρίσκω ἐν αὐτῷ αἰτίαν.
7 Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
ἀπεκρίθησαν αὐτῷ οἱ Ἰουδαῖοι· Ἡμεῖς νόμονἔχομεν, καὶ κατὰ τὸν ⸀νόμον ὀφείλει ἀποθανεῖν, ὅτι ⸂υἱὸν θεοῦ ἑαυτὸν ἐποίησεν.
8 Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi,
Ὅτε οὖν ἤκουσεν ὁ Πιλᾶτος τοῦτον τὸν λόγον, μᾶλλον ἐφοβήθη,
9 sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba.
καὶ εἰσῆλθεν εἰς τὸ πραιτώριον πάλιν καὶ λέγει τῷ Ἰησοῦ· Πόθεν εἶ σύ; ὁ δὲ Ἰησοῦς ἀπόκρισιν οὐκ ἔδωκεν αὐτῷ.
10 Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
λέγει οὖν αὐτῷ ὁ Πιλᾶτος· Ἐμοὶ οὐ λαλεῖς; οὐκ οἶδας ὅτι ἐξουσίαν ἔχω ⸂ἀπολῦσαί σε καὶ ἐξουσίαν ἔχω σταυρῶσαί σε;
11 Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
ἀπεκρίθη ⸀αὐτῷἸησοῦς· Οὐκ εἶχες ἐξουσίαν ⸂κατʼ ἐμοῦ οὐδεμίαν εἰ μὴ ἦν ⸂δεδομένον σοι ἄνωθεν· διὰ τοῦτο ὁ ⸀παραδούςμέ σοι μείζονα ἁμαρτίαν ἔχει.
12 Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
ἐκ τούτου ⸂ὁ Πιλᾶτος ἐζήτει ἀπολῦσαι αὐτόν· οἱ δὲ Ἰουδαῖοι ⸀ἐκραύγασανλέγοντες· Ἐὰν τοῦτον ἀπολύσῃς, οὐκ εἶ φίλος τοῦ Καίσαρος· πᾶς ὁ βασιλέα ἑαυτὸν ποιῶν ἀντιλέγει τῷ Καίσαρι.
13 Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata).
Ὁ οὖν Πιλᾶτος ἀκούσας ⸂τῶν λόγων τούτων ἤγαγεν ἔξω τὸν Ἰησοῦν, καὶ ἐκάθισεν ⸀ἐπὶβήματος εἰς τόπον λεγόμενον Λιθόστρωτον, Ἑβραϊστὶ δὲ Γαββαθα.
14 Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
ἦν δὲ παρασκευὴ τοῦ πάσχα, ὥρα ⸂ἦν ὡς ἕκτη. καὶ λέγει τοῖς Ἰουδαίοις· Ἴδε ὁ βασιλεὺς ὑμῶν.
15 Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
⸂ἐκραύγασαν οὖν ἐκεῖνοι· Ἆρον ἆρον, σταύρωσον αὐτόν. λέγει αὐτοῖς ὁ Πιλᾶτος· Τὸν βασιλέα ὑμῶν σταυρώσω; ἀπεκρίθησαν οἱ ἀρχιερεῖς· Οὐκ ἔχομεν βασιλέα εἰ μὴ Καίσαρα.
16 A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.
τότε οὖνπαρέδωκεν αὐτὸν αὐτοῖς ἵνα σταυρωθῇ. Παρέλαβον ⸀οὖν τὸν ⸀Ἰησοῦν·
17 Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota).
καὶ βαστάζων ⸂αὑτῷ τὸν σταυρὸν ἐξῆλθεν εἰς ⸀τὸνλεγόμενον Κρανίου Τόπον, ⸀ὃλέγεται Ἑβραϊστὶ Γολγοθα,
18 Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
ὅπου αὐτὸν ἐσταύρωσαν, καὶ μετʼ αὐτοῦ ἄλλους δύο ἐντεῦθεν καὶ ἐντεῦθεν, μέσον δὲ τὸν Ἰησοῦν.
19 Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.
ἔγραψεν δὲ καὶ τίτλον ὁ Πιλᾶτος καὶ ἔθηκεν ἐπὶ τοῦ σταυροῦ· ἦν δὲ γεγραμμένον· Ἰησοῦς ὁ Ναζωραῖος ὁ βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων.
20 Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik.
τοῦτον οὖν τὸν τίτλον πολλοὶ ἀνέγνωσαν τῶν Ἰουδαίων, ὅτι ἐγγὺς ἦν ὁ τόπος τῆς πόλεως ὅπου ἐσταυρώθη ὁ Ἰησοῦς· καὶ ἦν γεγραμμένον Ἑβραϊστί, ⸂Ῥωμαϊστί, Ἑλληνιστί⸃.
21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”
ἔλεγον οὖν τῷ Πιλάτῳ οἱ ἀρχιερεῖς τῶν Ἰουδαίων· Μὴ γράφε· Ὁ βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων, ἀλλʼ ὅτι ἐκεῖνος εἶπεν Βασιλεὺς ⸂τῶν Ἰουδαίων εἰμί.
22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”
ἀπεκρίθη ὁ Πιλᾶτος· Ὃ γέγραφα γέγραφα.
23 Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.
οἱ οὖν στρατιῶται ὅτε ἐσταύρωσαν τὸν Ἰησοῦν ἔλαβον τὰ ἱμάτια αὐτοῦ καὶ ἐποίησαν τέσσαρα μέρη, ἑκάστῳ στρατιώτῃ μέρος, καὶ τὸν χιτῶνα. ἦν δὲ ὁ χιτὼν ἄραφος, ἐκ τῶν ἄνωθεν ὑφαντὸς διʼ ὅλου·
24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce, “Suka rarraba tufafina a junansu, suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan.
εἶπαν οὖν πρὸς ἀλλήλους· Μὴ σχίσωμεν αὐτόν, ἀλλὰ λάχωμεν περὶ αὐτοῦ τίνος ἔσται· ἵνα ἡ γραφὴ πληρωθῇ ⸂ἡ λέγουσα· Διεμερίσαντο τὰ ἱμάτιά μου ἑαυτοῖς καὶ ἐπὶ τὸν ἱματισμόν μου ἔβαλον κλῆρον. Οἱ μὲν οὖν στρατιῶται ταῦτα ἐποίησαν.
25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin.
Εἱστήκεισαν δὲ παρὰ τῷ σταυρῷ τοῦ Ἰησοῦ ἡ μήτηρ αὐτοῦ καὶ ἡ ἀδελφὴ τῆς μητρὸς αὐτοῦ, Μαρία ἡ τοῦ Κλωπᾶ καὶ Μαρία ἡ Μαγδαληνή.
26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,”
Ἰησοῦς οὖν ἰδὼν τὴν μητέρα καὶ τὸν μαθητὴν παρεστῶτα ὃν ἠγάπα λέγει τῇ ⸀μητρί Γύναι, ⸀ἴδεὁ υἱός σου·
27 ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
εἶτα λέγει τῷ μαθητῇ· ⸀Ἴδεἡ μήτηρ σου. καὶ ἀπʼ ἐκείνης τῆς ὥρας ἔλαβεν ὁ μαθητὴς αὐτὴν εἰς τὰ ἴδια.
28 Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”
Μετὰ τοῦτο ⸀εἰδὼςὁ Ἰησοῦς ὅτι ⸂ἤδη πάντα τετέλεσται ἵνα τελειωθῇ ἡ γραφὴ λέγει· Διψῶ.
29 To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu.
⸀σκεῦοςἔκειτο ὄξους μεστόν· ⸂σπόγγον οὖν μεστὸν τοῦ ὄξους ⸀ὑσσώπῳπεριθέντες προσήνεγκαν αὐτοῦ τῷ στόματι.
30 Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
ὅτε οὖν ἔλαβεν τὸ ὄξος ὁ Ἰησοῦς εἶπεν· Τετέλεσται, καὶ κλίνας τὴν κεφαλὴν παρέδωκεν τὸ πνεῦμα.
31 To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan.
Οἱ οὖν Ἰουδαῖοι, ⸂ἐπεὶ παρασκευὴ ἦν, ἵνα μὴ μείνῃ ἐπὶ τοῦ σταυροῦ τὰ σώματα ἐν τῷ σαββάτῳ⸃, ἦν γὰρ μεγάλη ἡ ἡμέρα ἐκείνου τοῦ σαββάτου, ἠρώτησαν τὸν Πιλᾶτον ἵνα κατεαγῶσιν αὐτῶν τὰ σκέλη καὶ ἀρθῶσιν.
32 Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan.
ἦλθον οὖν οἱ στρατιῶται, καὶ τοῦ μὲν πρώτου κατέαξαν τὰ σκέλη καὶ τοῦ ἄλλου τοῦ συσταυρωθέντος αὐτῷ·
33 Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.
ἐπὶ δὲ τὸν Ἰησοῦν ἐλθόντες, ὡς εἶδον ⸂ἤδη αὐτὸν τεθνηκότα, οὐ κατέαξαν αὐτοῦ τὰ σκέλη,
34 A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito.
ἀλλʼ εἷς τῶν στρατιωτῶν λόγχῃ αὐτοῦ τὴν πλευρὰν ἔνυξεν, καὶ ⸂ἐξῆλθεν εὐθὺς αἷμα καὶ ὕδωρ.
35 Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata.
καὶ ὁ ἑωρακὼς μεμαρτύρηκεν, καὶ ἀληθινὴ ⸂αὐτοῦ ἐστιν ἡ μαρτυρία, καὶἐκεῖνος οἶδεν ὅτι ἀληθῆ λέγει, ἵνα ⸀καὶ ὑμεῖς ⸀πιστεύητε
36 Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,”
ἐγένετο γὰρ ταῦτα ἵνα ἡ γραφὴ πληρωθῇ· Ὀστοῦν οὐ συντριβήσεται ⸀αὐτοῦ
37 kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
καὶ πάλιν ἑτέρα γραφὴ λέγει· Ὄψονται εἰς ὃν ἐξεκέντησαν.
38 Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin.
Μετὰ ⸀δὲταῦτα ἠρώτησεν τὸν Πιλᾶτον Ἰωσὴφ ⸀ἀπὸἉριμαθαίας, ὢν μαθητὴς τοῦ Ἰησοῦ κεκρυμμένος δὲ διὰ τὸν φόβον τῶν Ἰουδαίων, ἵνα ἄρῃ τὸ σῶμα τοῦ Ἰησοῦ· καὶ ἐπέτρεψεν ὁ Πιλᾶτος. ἦλθεν οὖν καὶ ἦρεν τὸ σῶμα ⸀αὐτοῦ
39 Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari.
ἦλθεν δὲ καὶ Νικόδημος, ὁ ἐλθὼν πρὸς ⸀αὐτὸννυκτὸς τὸ πρῶτον, φέρων ⸀μίγμασμύρνης καὶ ἀλόης ὡς λίτρας ἑκατόν.
40 Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza.
ἔλαβον οὖν τὸ σῶμα τοῦ Ἰησοῦ καὶ ἔδησαν ⸀αὐτὸὀθονίοις μετὰ τῶν ἀρωμάτων, καθὼς ἔθος ἐστὶν τοῖς Ἰουδαίοις ἐνταφιάζειν.
41 A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba.
ἦν δὲ ἐν τῷ τόπῳ ὅπου ἐσταυρώθη κῆπος, καὶ ἐν τῷ κήπῳ μνημεῖον καινόν, ἐν ᾧ οὐδέπω οὐδεὶς ⸂ἦν τεθειμένος·
42 Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.
ἐκεῖ οὖν διὰ τὴν παρασκευὴν τῶν Ἰουδαίων, ὅτι ἐγγὺς ἦν τὸ μνημεῖον, ἔθηκαν τὸν Ἰησοῦν.