< Yohanna 17 >
1 Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce, “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka.
Yeshua said these things, and lifting up his eyes to heaven, he said, "Father, the time has come. Glorify your Son, that your Son may also glorify you;
2 Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. (aiōnios )
even as you gave him authority over all flesh, he will give everlasting life to all whom you have given him. (aiōnios )
3 Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. (aiōnios )
This is everlasting life, that they may know you, the only true God, and him whom you sent, Yeshua Meshikha. (aiōnios )
4 Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni.
I glorified you on the earth by accomplishing the work which you have given me to do.
5 Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.
Now, Father, glorify me with your own self with the glory which I had with you before the world existed.
6 “Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka.
I revealed your name to the people whom you have given me out of the world. They were yours, and you have given them to me. They have kept your word.
7 Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito.
Now they have known that all things whatever you have given me are from you,
8 Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni.
for the words which you have given me I have given to them, and they received them, and knew for sure that I came forth from you, and they have believed that you sent me.
9 Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne.
I pray for them. I do not pray for the world, but for those whom you have given me, for they are yours.
10 Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu.
All things that are mine are yours, and yours are mine, and I am glorified in them.
11 Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.
I am no more in the world, but they are in the world, and I am coming to you. Holy Father, keep them through your name which you have given me, that they may be one, even as we are.
12 Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
While I was with them, I kept them in your name which you have given me, and I guarded them, and not one of them perished, except the son of destruction, that the Scripture might be fulfilled.
13 “Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu.
But now I come to you, and I say these things in the world, that they may have my joy made full in themselves.
14 Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.
I have given them your word. The world hated them, because they are not of the world, even as I am not of the world.
15 Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
I pray not that you would take them from the world, but that you would keep them from the evil one.
16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.
They are not of the world even as I am not of the world.
17 Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.
Sanctify them in the truth. Your word is truth.
18 Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya.
As you sent me into the world, even so I have sent them into the world.
19 Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.
For their sakes I sanctify myself, that they themselves also may be sanctified in truth.
20 “Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu.
Not for these only do I pray, but for those also who believe in me through their word,
21 Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni.
that they may all be one; even as you, Father, are in me, and I in you, that they also may be in us; that the world may believe that you sent me.
22 Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.
The glory which you have given me, I have given to them; that they may be one, even as we are one;
23 Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.
I in them, and you in me, that they may be perfected into one; that the world may know that you sent me, and loved them, even as you loved me.
24 “Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya.
Father, I desire that they also whom you have given me be with me where I am, that they may see my glory, which you have given me, for you loved me before the foundation of the world.
25 “Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni.
Righteous Father, the world hasn't known you, but I knew you; and these knew that you sent me.
26 Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”
I made known to them your name, and will make it known; that the love with which you loved me may be in them, and I in them."