< Yohanna 16 >
1 “Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe.
“我把这一切告诉了你们,让你们不会放弃对我的信任。
2 Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.
人们会把你们赶出会堂,事实上时间已到,所有要杀害你们的人,都以为这样就是侍奉上帝。
3 Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba.
他们这样做是因为他们不认识天父,也不认识我。我把一切告诉你们,以便在这一切发生的时候,你们会记得我所说的话。
4 Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.
我无需在开始就告诉你们这一切,因为你们将跟随我。
5 “Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’
但现在我将要到派我来此的天父那里,但你们没有人问:‘你要到哪里去?’
6 Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki.
当然了,现在我把这一切都告诉了你们,你们便心生悲伤。
7 Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.
但说实话,我的离开对你们更好。如果我不离开,保惠师就不会到来。我若离开,我就会派他来到你们身边。
8 Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci,
他到来的时候,就会说服世人,他们关于罪恶和正义的看法是错的,就会告诉他们什么是审判。
9 a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba;
关于罪,是因为他们不信我;
10 a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba;
关于义,是因为我到父那里去,你们就再看不见我;
11 a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.
关于审判,是因为这世界的统治者已经受了审判。
12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba.
我还有许多事要告诉你们,可是你们现在无法承受;
13 Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.
只等真理圣灵来到,他会教导你们一切真理。他不是为自己说话,而是把他听见的都说出来,把将来的事告诉你们。
14 Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku.
他让我荣耀,因为他要把从我那里获得的都告诉你们。
15 Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’”
属于天父的一切也都属于我,所以我说,圣灵会把从我这里获得的告诉你们。
16 Yesu ya ci gaba da cewa, “Jim kaɗan, ba za ku ƙara ganina ba, sa’an nan bayan an jima kaɗan kuma, za ku gan ni.”
不久后,你们不会再看见我,但再过一段时间,你们还要看见我。”
17 A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?”
于是他的门徒中有几个彼此说:“他对我们说:‘不久后,你们就不会再看见我,但再过一段时间,你们还要看见我。’又说:‘因为我要到天父那里去。’这是什么意思呢?”
18 Suka yi ta tambaya, “Me yake nufi da ‘jim kaɗan’? Ba mu fahimci abin da yake faɗi ba.”
他们又说:“他所说的‘不久’,是什么意思呢?不理解他在讲什么。”
19 Yesu ya gane suna so su tambaye shi game da wannan, sai ya ce musu, “Kuna tambayar juna game da abin da nake nufi da na ce, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, da kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni’?
耶稣知道他们想问他,就说:“我所说的‘不久,你们不会看见我,但再过一段时间,你们还要看见我’,你们为了这话彼此议论吗?
20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.
告诉你们实话,你们会痛哭哀号,世人却要欢喜,你们会忧愁,但你们的忧愁要变为欢乐。
21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya.
妇人生产的时候会痛苦,因为这是分娩的时候。但生了孩子以后,就不再记住那痛苦了,而是欢喜孩子的诞生。
22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.
是的,现在你们也会悲伤,但我会与你们再次相见,你们的心就会欢喜,没有人能夺走你们的欢喜。
23 A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana.
到了那天,你们什么也不会问我了。告诉你们实话,以我的名向天父求的任何事,他必定给予你们。
24 Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.
你们一直以来没有以我的名求什么,现在你们祈求就必然应验,让你们的欢喜圆满。
25 “Ko da yake ina magana da misalai, lokaci yana zuwa da ba zan ƙara yin magana da misalai ba, sai dai in faɗa muku a fili game da Ubana.
我一直用比喻向你们讲述,但很快,我不会再使用比喻,而是把关于天父的事明明白白讲出来。
26 A ranan nan, za ku roƙa a cikin sunana. Ban ce zan roƙi Uba a madadinku ba.
到了那天,你们要以我的名祈求,我不是说我要以你们的名义请求天父,
27 Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito.
因为天父爱你们,因为你们爱我,并且相信我来自上帝。
28 Na fito daga wurin Uba, na kuma shigo duniya, yanzu kuwa zan bar duniya in koma wurin Uba.”
我离开天父来到这世界,现在我要离开这世界,到天父那里去。”
29 Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba.
门徒说:“现在你就明说了,不再用比喻,
30 Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.”
现在我们很确定你无所不知,为了知道人们在想什么问题,你不需要问他们。因此,我们信你来自上帝。”
31 Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata!
耶稣对他们说:“现在你们真信吗?
32 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.
时候要到了,其实已经到了,你们要分散到各自该去的地方,留我独自一个人。其实我不是独自一个人,因为有天父与我同在。
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
我把这些事告诉你们,是要使你们因为与我一体而平安。 在世上你们会遭受苦难,但你们要勇敢,我已经胜过了这世界!”