< Yohanna 15 >

1 “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.
I am the True Vine, and my Father is the Vine-grower.
2 Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da’ya’ya, domin yă ƙara ba da’ya’ya.
Any unfruitful branch in me he takes away, and he cleanses every fruitful branch, that it may bear more fruit.
3 Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.
You are already clean because of the Message that I have given you.
4 Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
Remain united to me, and I will remain united to you. As a branch cannot bear fruit by itself, unless it remains united to the vine; no more can you, unless you remain united to me.
5 “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
I am the Vine, you are the branches. He that remains united to me, while I remain united to him — he bears fruit plentifully; for you can do nothing apart from me.
6 Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.
If any one does not remain united to me, he is thrown away, as a branch would be, and withers up. Such branches are collected and thrown into the fire, and are burnt.
7 In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.
If you remain united to me, and my teaching remains in your hearts, ask whatever you wish, and it shall be yours.
8 Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
It is by your bearing fruit plentifully, and so showing yourselves my disciples, that my Father is honoured.
9 “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata.
As the Father has loved me, so have I loved you; remain in my love.
10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.
If you lay my commands to heart, you will remain in my love; just as I have laid the Father’s commands to heart and remain in his love.
11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.
I have told you all this so that my own joy may be yours, and that your joy may be complete.
12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
This is my command — Love one another, as I have loved you.
13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
No one can give greater proof of love than by laying down his life for his friends.
14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.
And you are my friends, if you do what I command you.
15 Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.
I no longer call you ‘servants,’ because a servant does not know what his master is doing; but I have given you the name of ‘friends,’ because I made known to you everything that I learned from my Father.
16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.
It was not you who chose me, but I who chose you, and I appointed you to go and bear fruit — fruit that should remain, so that the Father might grant you whatever you ask in my Name.
17 Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
I am giving you these commands that you may love one another.
18 “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.
If the world hates you, you know that it has first hated me.
19 Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
If you belonged to the world, the world would love its own. Because you do not belong to the world, but I have chosen you out of the world — that is why the world hates you.
20 Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.
Remember what I said to you — ‘A servant is not greater than his master.’ If they have persecuted me, they will also persecute you; if they have laid my Message to heart, they will lay yours to heart also.
21 Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba.
But they will do all this to you, because you believe in my Name, for they do not know him who sent me.
22 Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu.
If I had not come and spoken to them, they would have had no sin to answer for; but as it is, they have no excuse for their sin.
23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma.
He who hates me hates my Father also.
24 Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana.
If I had not done among them such work as no one else ever did, they would have had no sin to answer for; but, as it is, they have both seen and hated both me and my Father.
25 Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’
And so is fulfilled what is said in their Law — ‘They hated me without cause.’
26 “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.
But, when the Helper comes, whom I will send to you from the Father — the Spirit of Truth, who comes from the Father — he will bear testimony to me;
27 Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.
yes, and you also are to bear testimony, because you have been with me from the first.

< Yohanna 15 >