< Yohanna 12 >
1 Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya tā da daga matattu.
2 A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi.
3 Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.
4 Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce,
5 “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.”
6 Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.
7 Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata.
8 Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”
9 Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya tā da daga matattu.
10 Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma,
11 gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.
12 Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima.
13 Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”
14 Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,
15 “Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona; duba, ga sarkinki yana zuwa, zaune a kan aholaki jaki.”
16 Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.
17 Taron da suke tare da shi a sa’ad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma tā da shi daga matattu suka yi ta baza labarin.
18 Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi.
19 Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu ko’ina. Ga shi, duk duniya tana bin sa!”
20 To, akwai waɗansu Hellenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin.
21 Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yă daɗe, muna so mu ga Yesu.”
22 Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.
23 Yesu ya amsa ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.
24 Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da’ya’ya da yawa.
25 Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami. (aiōnios )
26 Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.
27 “Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo.
28 Uba, ka ɗaukaka sunanka!” Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.”
29 Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce mala’ika ne ya yi masa magana.
30 Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba.
31 Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan.
32 Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.”
33 Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi.
34 Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?” (aiōn )
35 Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba.
36 Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama’ya’yan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.
37 Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba.
38 Wannan ya faru ne, don a cika maganar annabi Ishaya cewa, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu, ga wa kuma aka bayyana hannun ikon Ubangiji?”
39 Saboda haka ba su iya gaskatawa ba, domin, kamar yadda Ishaya ya faɗa a wani wuri cewa,
40 “Ya makantar da idanunsu ya kuma taurare zukatansu, don kada su gani da idanunsu, ko su fahimta a zukatansu, ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”
41 Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.
42 Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi. Amma saboda Farisiyawa ba su furta bangaskiyarsu ba, don tsoron kada a kore su daga majami’a;
43 gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah.
44 Sa’an nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.
45 Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne.
46 Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu.
47 “Duk mai jin kalmomina bai kuwa kiyaye su ba, ba ni ba ne nake shari’anta shi. Gama ban zo domin in yi wa duniya shari’a ba, sai dai domin in cece ta.
48 Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe.
49 Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi.
50 Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.” (aiōnios )