< Yohanna 11 >
1 To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da’yar’uwarta Marta.
Now a certain man was sick, Lazarus, of Bethany, the village of Mary and Martha her sister.
2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta.
It was the Mary that anointed the Lord with ointment, and wiped his feet with her hair, whose brother Lazarus was sick.
3 Saboda haka’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
Therefore his sisters sent to him, saying: Lord, behold, he whom thou lovest is sick.
4 Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.”
But when Jesus heard it, he said: This sickness is not to death, but for the glory of God, that by it the Son of God may be glorified.
5 Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da’yar’uwarta da kuma Lazarus.
Now, Jesus loved Martha, and her sister, and Lazarus.
6 Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
When, therefore, he heard that he was sick, he still remained two days in the place where he was.
7 Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.”
Then after this, he said to his disciples: Let us go into Judea again.
8 Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
His disciples said to him: Rabbi, the Jews just now sought to stone thee, and art thou going thither again?
9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan.
Jesus answered: Are there not twelve hours in the day? If any one walks during the day, he does not stumble, for he sees the light of this world.
10 Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”
But if any one walks in the night, he stumbles, because there is no light in him.
11 Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
Thus spoke he; and after this he said to them: Our friend Lazarus sleeps; but I go that I may awake him out of sleep.
12 Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.”
Then his disciples said: Lord, if he sleeps, he will be saved.
13 Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
Jesus spoke of his death; but they thought that he spoke of taking rest in sleep.
14 Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu,
Therefore, Jesus then said to them plainly: Lazarus is dead.
15 amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.”
And I rejoice, on your account, that I was not there, in order that you may believe. But let us go to him.
16 Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
Then Thomas, who is called Didymus, said to his fellow-disciples: Let us also go, that we may die with him.
17 Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari.
Then when Jesus came, he found that he had already been four days in the tomb.
18 Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima,
Now Bethany was near Jerusalem, about fifteen furlongs off.
19 Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu.
And many of the Jews had come to Martha and Mary, to comfort them concerning their brother.
20 Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
Then Martha, when she heard that Jesus was coming, went out to meet him; but Mary sat still in the house.
21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.
Then Martha said to Jesus: Lord, if thou hadst been here my brother would not have died.
22 Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
But even now, I know that whatever thou wilt ask of God, God will give thee.
23 Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.”
Jesus said to her: Your brother shall rise again.
24 Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
Martha said to him: I know that he will rise, in the resurrection at the last day.
25 Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;
Jesus said to her: I am the resurrection, and the life; he that believes on me, though he were dead, yet shall he live;
26 kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?” (aiōn )
and he that lives and believes on me, shall never die. Do you believe this? (aiōn )
27 Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
She said to him: Yes, Lord; I believe that thou art the Christ, the Son of God, who was to come into the world.
28 Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.”
And when she had said this, she went away, and called Mary, her sister, secretly, saying: The Teacher has come, and calls for you.
29 Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa.
When she heard it, she rose quickly and came to him.
30 Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi.
Now Jesus had not yet come into the village, but was in the place where Martha met him.
31 Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
Then the Jews that were with her in the house, and were comforting her, seeing Mary rise and go out quickly, followed her, saying: She is going to the tomb to weep there.
32 Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
Then, when Mary came where Jesus was, and saw him, she fell at his feet, saying to him: Lord, if thou hadst been here, my brother would not have died.
33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu.
Then, when Jesus saw her weeping, and the Jews that came with her weeping also, he was greatly moved in spirit, and troubled;
34 Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
and he said: Where have you laid him? They said to him: Lord, come and see.
36 Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
Then said the Jews: See how he loved him!
37 Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”
And some of them said: Could not he, who opened the eyes of the blind man, have caused that even this man should not have died?
38 Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse.
Then Jesus, again greatly moved within himself, came to the tomb. It was a cave, and a stone was laid against it.
39 Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta,’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”
Jesus said: Take away the stone. Martha, the sister of him that was dead, said to him: Lord, the body is offensive; for he has been dead four days.
40 Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”
Jesus said to her: Did I not tell you, that, if you would believe, you should see the glory of God?
41 Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni.
Then they took away the stone. And Jesus lifted up his eyes and said: Father, I thank thee, that thou hast heard me.
42 Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
I know, in deed, that thou dost always hear me. But for the sake of the multitude who stand around me, I have said it, that they may believe that thou hast sent me.
43 Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”
And when he had said these things, he cried with a loud voice, Lazarus, come forth.
44 Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”
And he that had been dead came forth, bound hand and foot with grave-clothes; and his face was bound around with a handkerchief. Jesus said to them: Loose him, and let him go.
45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.
Then many of the Jews that had come to Mary, and who saw what he had done, believed on him.
46 Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
But some of them went away to the Pharisees, and told them what Jesus had done.
47 Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
Then the chief priests and the Pharisees called together the Sanhedrin, and said: What are we doing? For this man does many signs.
48 In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
If we thus let him alone, all will believe on him, and the Romans will come and take away our place and our nation.
49 Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!
But one of them, Caiaphas, who was chief priest that year, said to them: You know nothing,
50 Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
nor do you consider that it is profitable for us, that one man should die for the people, and not that the whole nation should perish.
51 Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,
But this he did not speak of himself; but being chief priest that year, he prophesied that Jesus was about to die for the nation;
52 ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.
and not for the nation only, but that he should gather into one the children of God that were scattered abroad.
53 Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
From that day, therefore, they consulted together to put him to death.
54 Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
Therefore, Jesus no longer walked openly among the Jews, but withdrew thence to the region near the wilderness, to a city called Ephraim, and there he remained with his disciples.
55 Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa.
And the passover of the Jews was near; and many went up from the country to Jerusalem, before the passover, to purify themselves.
56 Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?”
Then they sought for Jesus, and said one to another, as they stood in the temple: What think you, that he will not come to the feast?
57 Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.
Now the chief priests and the Pharisees had given orders, that, if any one knew where he was, he should inform them, that they might take him.