< Yohanna 10 >

1 “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.
Most assuredly, I say to you, he who enters not by the gate into the sheepfold, but climbs over the fence, is a thief and a robber.
2 Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.
The shepherd always enters by the gate.
3 Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje.
To him, the porter opens, and the sheep obey his voice. His own sheep he calls by name, and leads out.
4 Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.
And having put out his sheep, he walks before them, and they follow him; because they know his voice.
5 Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”
They will not follow a stranger, but flee from him; because they know not the voice of strangers.
6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.
Jesus addressed this similitude to them, but they did not comprehend what he said.
7 Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.
He therefore added, Most assuredly, I say to you, I am the gate of the fold.
8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne,’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba.
All who preceded me were thieves and robbers; but the sheep obeyed them not.
9 Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo.
I am the gate: such as enter by me shall be safe: they shall go in and out, and find pasture.
10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
The thief comes in only to steal, to slay, and to destroy. I am come that they may have life, and have it abundantly.
11 “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.
I am the good shepherd. The good shepherd gives his life for his sheep.
12 Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.
The hireling, who is not the shepherd, and to whom the sheep do not belong, when he sees the wolf coming, abandons the sheep, and flees; and the wolf tears them, and disperses the flock.
13 Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.
The hireling flees, because he is a hireling, and cares not for the sheep.
14 “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni,
I am the good shepherd. And I know my own, and am known by them,
15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.
(even as the Father knows me, and I know the Father; ) and I give my life for the sheep.
16 Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.
I have other sheep, besides, which are not of this fold. Them I must also bring; and they will obey my voice; and there shall be one flock, one shepherd.
17 Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.
For this the Father loves me, because I give my life, to be afterward resumed.
18 Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”
No one forces it from me: but I give it of myself. I have power to give it, and I have power to resume it. This commandment I have received from my Father.
19 Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa.
Again there was a division among the Jews, occasioned by this discourse.
20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”
Many of them said, He has a demon, and is mad: why do you hear him?
21 Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”
Others said, These are not the words of a demonise. Can a demon give sight to the blind?
22 Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa.
Afterward, when they were celebrating the feast of the dedication, at Jerusalem,
23 Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon,
it being in winter; as Jesus walked in the temple, in Solomon's portico,
24 sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”
the Jews surrounding him, said to him, How long will you keep us in suspense? If you be the Messiah, tell us plainly.
25 Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.
Jesus answered, I told you; but you believed not. The works which I do in my Father's name, testify of me.
26 Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
But you believe not, for you are not of my sheep.
27 Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.
My sheep, as I told you, obey my voice; I know them, and they follow me.
28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. (aiōn g165, aiōnios g166)
Besides, I give them eternal life; and they shall never perish, neither shall any one wrest them out of my hands. (aiōn g165, aiōnios g166)
29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.
My Father, who gave them me, is greater than all; and none can wrest them out of my Father's hand.
30 Da ni da Uba ɗaya ne.”
I and the Father are one.
31 Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi,
Then the Jews again took up stones to stone him.
32 amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”
Jesus said to them, Many good works I have shown you from my Father; for which of these works do you stone me?
33 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”
The Jews answered, For a good work we do not stone you, but for blasphemy; because you, being a man, make yourself God.
34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?
Jesus replied, Is it not written in your law, "I said, You are gods?"
35 Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’
If the law styled them gods, to whom the word of God was addressed, and if the language of scripture in unexceptionable;
36 to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’
do you charge him with blasphemy whom the Father has consecrated his Apostle to the world, for calling himself his Son?
37 In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.
If I do not the works of my Father, believe me not.
38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.”
But if I do, though you believe not me, believe the works, that you may know and believe, that the Father is in me, and I am in him.
39 Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.
They then attempted again to seize him; but he escaped out of their hands,
40 Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna
and retired again toward the Jordan, and abode in the place where John first immersed.
41 mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”
And many resorted to him, who said, John, indeed, wrought no miracle: but all that John spoke of this man, is true.
42 A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.
And many believed on him there.

< Yohanna 10 >