< Yowel 1 >
1 Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.
2 Ku ji wannan, ku dattawa, ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar. Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin kakanninku?
3 Ku faɗa wa’ya’yanku, bari kuma’ya’yanku su faɗa wa’ya’yansu,’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.
4 Abin da ɗango ya bari fāri masu girma sun cinye; abin da fāri masu girma suka bari, burduduwa ta cinye; abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.
5 Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka! Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi; ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi, gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.
6 Wata al’umma ta mamaye ƙasata, tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa; tana da haƙoran zaki, da zagar zakanya.
7 Ta mayar da kuringar inabina kango ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena. Ta ɓamɓare bayansu duka ta kuma jefar da su ta bar rassansu fari fat.
8 Ku yi makoki kamar budurwa a cikin tsummoki tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.
9 Hadayun hatsi da hadayun sha an yanke su daga gidan Ubangiji. Firistoci suna makoki, su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.
10 Filaye sun zama marasa amfani, ƙasa ta bushe; an lalatar da hatsi, sabon ruwan inabin ya bushe, mai kuma ba amfani.
11 Ku fid da zuciya, ku manoma, ku yi ihu, ku masu noma inabi; ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, saboda an lalata girbin filaye.
12 Kuringar inabin ta bushe itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, dukan itatuwan filaye, sun bushe. Tabbatacce farin cikin’yan adam ya bushe.
13 Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki; ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade. Zo, ku kwana saye da tsummoki, ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima, gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha daga gidan Allahnku.
14 Ku yi shelar azumi mai tsarki; ku kira tsarkakan taro. Ku kira dattawa da kuma dukan mazaunan ƙasar zuwa gidan Ubangiji Allahnku, ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
15 Kaito saboda wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.
16 Ba a yanke abinci a idanunmu, farin ciki da kuma murna daga gidan Allahnmu ba?
17 Iri suna ta yanƙwanewa a busasshiyar ƙasa Ɗakunan ajiya sun lalace, an rurrushe rumbunan hatsin, gama hatsi ya ƙare.
18 Ji yadda dabbobi suke nishi! Garkunan shanu sun ruɗe saboda ba su da ciyawa, har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
19 A gare ka, ya Ubangiji, nake kira, gama wuta ta cinye wurin kiwo harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
20 Har ma namun jeji suna haki gare ka; rafuffuka sun bushe wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.