< Ayuba 9 >

1 Sai Ayuba ya amsa,
Then Job answered:
2 “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
“Yes, I know that it is so, but how can a mortal be righteous before God?
3 Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.
If one wished to contend with God, he could not answer Him one time out of a thousand.
4 Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?
God is wise in heart and mighty in strength. Who has resisted Him and prospered?
5 Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.
He moves mountains without their knowledge and overturns them in His anger.
6 Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta.
He shakes the earth from its place, so that its foundations tremble.
7 Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.
He commands the sun not to shine; He seals off the stars.
8 Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.
He alone stretches out the heavens and treads on the waves of the sea.
9 Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.
He is the Maker of the Bear and Orion, of the Pleiades and the constellations of the south.
10 Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.
He does great things beyond searching out, and wonders without number.
11 Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.
Were He to pass by me, I would not see Him; were He to move, I would not recognize Him.
12 Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’
If He takes away, who can stop Him? Who dares to ask Him, ‘What are You doing?’
13 Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.
God does not restrain His anger; the helpers of Rahab cower beneath Him.
14 “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?
How then can I answer Him or choose my arguments against Him?
15 Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.
For even if I were right, I could not answer. I could only beg my Judge for mercy.
16 Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.
If I summoned Him and He answered me, I do not believe He would listen to my voice.
17 Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.
For He would crush me with a tempest and multiply my wounds without cause.
18 Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.
He does not let me catch my breath, but overwhelms me with bitterness.
19 In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?
If it is a matter of strength, He is indeed mighty! If it is a matter of justice, who can summon Him?
20 Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.
Even if I were righteous, my mouth would condemn me; if I were blameless, it would declare me guilty.
21 “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.
Though I am blameless, I have no concern for myself; I despise my own life.
22 Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’
It is all the same, and so I say, ‘He destroys both the blameless and the wicked.’
23 Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.
When the scourge brings sudden death, He mocks the despair of the innocent.
24 Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?
The earth is given into the hand of the wicked; He blindfolds its judges. If it is not He, then who is it?
25 “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.
My days are swifter than a runner; they flee without seeing good.
26 Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.
They sweep by like boats of papyrus, like an eagle swooping down on its prey.
27 ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’
If I were to say, ‘I will forget my complaint and change my expression and smile,’
28 duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.
I would still dread all my sufferings; I know that You will not acquit me.
29 Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.
Since I am already found guilty, why should I labor in vain?
30 Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,
If I should wash myself with snow and cleanse my hands with lye,
31 duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.
then You would plunge me into the pit, and even my own clothes would despise me.
32 “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.
For He is not a man like me, that I can answer Him, that we can take each other to court.
33 In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare,
Nor is there a mediator between us, to lay his hand upon us both.
34 wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.
Let Him remove His rod from me, so that His terror will no longer frighten me.
35 Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.
Then I would speak without fear of Him. But as it is, I am on my own.

< Ayuba 9 >