< Ayuba 8 >
1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
2 “Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa? Maganganunka ba su da amfani.
3 Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba?
4 Lokacin da’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa.
5 Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki,
6 in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka.
7 Ko da yake za ka fara da kaɗan, duk da haka za ka gama da samu mai yawa.
8 “Tambayi na gaba da kai ka ji abin da iyayenka suka koya
9 gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba, kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne.
10 Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba? Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba?
11 Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?
12 Yayinda take girma ba a yanka ta, takan mutu da sauri fiye da ciyawa.
13 Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.
14 Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi; abin da yake dogara a kai yanar gizo ce.
15 Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi, sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba.
16 Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai, tana yaɗuwa da kyau;
17 shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu, suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu.
18 Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take, wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’
19 Ba shakka shukar ta mutu ke nan, kuma waɗansu za su tsiro a wurin.
20 “Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta.
21 Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna.
22 Maƙiyanka za su sha kunya, za a kawar da tentin mugaye.”