< Ayuba 6 >
1 Sa’an nan Ayuba ya amsa,
Then Job answered and said:
2 “Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!
O that my grief were weighed thoroughly! That my calamities were put together in the balance!
3 Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka.
Surely they would be heavier than the sand of the sea; On this account were my words rash.
4 Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.
For the arrows of the Almighty have pierced me; Their poison drinketh up my spirit; The terrors of God set themselves in array against me.
5 Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?
Doth the wild ass bray in the midst of grass? Or loweth the ox over his fodder?
6 Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?
Can that which is unsavory be eaten without salt? Is there any taste in the white of an egg?
7 Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.
That which my soul abhorreth to touch Hath become my loathsome food.
8 “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata,
O that I might have my request, And that God would grant me that which I long for!
9 wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina!
That it would please God to destroy me; That he would let loose his hand, and make an end of me!
10 Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.
Yet it should still be my consolation, Yea, in unsparing anguish I would exult, That I have not denied the commands of the Holy One.
11 “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?
What is my strength, that I should hope? And what mine end, that I should be patient?
12 Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne?
Is my strength the strength of stones? Or is my flesh brass?
13 Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni?
Alas, there is no help within me! Deliverance is driven from me!
14 “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
To the afflicted, kindness should be shown by a friend; Else he casteth off the fear of the Almighty.
15 Amma’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,
But my brethren are faithless like a brook; Like streams of the valley that pass away;
16 kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,
Which are turbid by reason of the ice, And the snow, which hideth itself in them.
17 amma da rani sai yă bushe, lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.
As soon as they flow forth, they vanish; When the heat cometh, they are dried up from their place.
18 Ayari sukan bar hanyarsu; sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.
The caravans turn aside to them on their way; They go up into the desert, and perish.
19 Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.
The caravans of Tema look for them; The companies of Sheba expect to see them;
20 Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai; sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.
They are ashamed that they have relied on them; They come to their place, and are confounded.
21 Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako; kun ga abin bantsoro kuka tsorata.
So ye also are nothing; Ye see a terror, and shrink back.
22 Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina, ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,
Have I said, Bring me gifts? Or, Give a present for me out of your substance?
23 ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina, ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?
Or, Deliver me from the enemy's hand? Or, Rescue me from the hand of the violent?
24 “Ku koya mini, zan yi shiru; ku nuna mini inda ban yi daidai ba.
Convince me, and I will hold my peace; Cause me to understand wherein I have erred.
25 Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?
How powerful are the words of truth! But what do your reproaches prove?
26 Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne, ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?
Do ye mean to censure words? The words of a man in despair are but wind.
27 Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku.
Truly ye spread a net for the fatherless; Ye dig a pit for your friend.
28 “Amma yanzu ku dube ni da kyau, zan yi muku ƙarya ne?
Look now upon me, I pray you; For to your very face can I speak falsehood?
29 Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi; ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi.
Return, I pray, and let there be no unfairness; Yea, return; —still is my cause righteous.
30 Ko akwai wata mugunta a bakina? Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?
Is there iniquity on my tongue? Cannot my taste discern what is sinful?