< Ayuba 42 >
1 Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
2 “Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa; ba wanda zai iya ɓata shirinka.
3 Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’ Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba, abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata.
4 “Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana zan tambaye ka, kuma za ka amsa mini.’
5 Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka.
6 Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.”
7 Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.
8 Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.”
9 Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.
10 Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.
11 Dukan’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.
12 Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.
13 Ya kuma haifi’ya’ya maza bakwai, mata uku.
14 ’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk.
15 Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta’yan’uwansu maza.
16 Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga’ya’yansa da’ya’yansu har tsara ta huɗu.
17 Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.