< Ayuba 41 >
1 “Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya?
2 Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?
3 Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali?
4 Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?
5 Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?
6 ’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu?
7 Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu?
8 In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!
9 Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne.
10 Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?
11 Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.
12 “Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.
13 Wa zai iya tuɓe mata mayafinta? Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta.
14 Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta? Haƙoranta ma abin tsoro ne?
15 An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai.
16 Suna kurkusa da juna yadda da ƙyar iska take iya wucewa tsakani.
17 An haɗa su da juna sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba.
18 Numfashinta yana fitar da wuta; idanunta kamar hasken zuwan safe.
19 Wuta tana fitowa daga bakinta; tartsatsin wuta suna fitowa,
20 Hayaƙi yana fitowa daga hancinta kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.
21 Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta.
22 Akwai ƙarfi a cikin wuyanta; razana tana wucewa a gabanta.
23 Namanta yana da kauri a manne da juna; naman yana da tauri ba ya matsawa.
24 Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse, da ƙarfi kamar dutsen niƙa.
25 Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata; suna ja da baya.
26 Takobi ba ta iya yankanta, kibiya ko māshi ba sa iya huda ta.
27 Ƙarfe kamar kara ne a wurinta tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta.
28 Māsu ba su sa ta tă gudu; jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta.
29 Kulki a gare ta kamar ciyawa ne, tana dariyar wucewar māshi.
30 Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya.
31 Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.
32 A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa.
33 Ba wani abu kamar ta a duniya, halitta marar tsoro.
34 Tana rena duk masu girman kai. Ita take mulki kan duk masu girman kai.”