< Ayuba 40 >

1 Ubangiji ya ce wa Ayuba,
And Jehovah doth answer Job, and saith: —
2 “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”
Is the striver with the Mighty instructed? The reprover of God, let him answer it.
3 Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
And Job answereth Jehovah, and saith: —
4 “Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna.
Lo, I have been vile, What do I return to Thee? My hand I have placed on my mouth.
5 Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”
Once I have spoken, and I answer not, And twice, and I add not.
6 Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,
And Jehovah answereth Job out of the whirlwind, and saith: —
7 “Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini.
Gird, I pray thee, as a man, thy loins, I ask thee, and cause thou Me to know.
8 “Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?
Dost thou also make void My judgment? Dost thou condemn Me, That thou mayest be righteous?
9 Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?
And an arm like God hast thou? And with a voice like Him dost thou thunder?
10 Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma, ka yafa daraja da muƙami.
Put on, I pray thee, excellency and loftiness, Yea, honour and beauty put on.
11 Ka saki fushinka, ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi.
Scatter abroad the wrath of thine anger, And see every proud one, and make him low.
12 Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya.
See every proud one — humble him, And tread down the wicked in their place.
13 Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.
Hide them in the dust together, Their faces bind in secret.
14 Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka.
And even I — I do praise thee, For thy right hand giveth salvation to thee.
15 “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.
Lo, I pray thee, Behemoth, that I made with thee: Grass as an ox he eateth.
16 Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta.
Lo, I pray thee, his power [is] in his loins, And his strength in the muscles of his belly.
17 Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.
He doth bend his tail as a cedar, The sinews of his thighs are wrapped together,
18 Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.
His bones [are] tubes of brass, His bones [are] as a bar of iron.
19 Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.
He [is] a beginning of the ways of God, His Maker bringeth nigh his sword;
20 Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa.
For food do mountains bear for him, And all the beasts of the field play there.
21 Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama.
Under shades he lieth down, In a secret place of reed and mire.
22 Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
Cover him do shades, [with] their shadow, Cover him do willows of the brook.
23 Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.
Lo, a flood oppresseth — he doth not haste, He is confident though Jordan Doth come forth unto his mouth.
24 Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?
Before his eyes doth [one] take him, With snares doth [one] pierce the nose?

< Ayuba 40 >