< Ayuba 4 >
1 Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
2 “In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru?
3 Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi.
4 Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu.
5 Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.
6 Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka?
7 “Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka? Ko an taɓa hallaka masu adalci?
8 Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta.
9 A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su.
10 Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki.
11 Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci,’ya’yan zakanya kuma sun watse.
12 “Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji.
13 Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.
14 Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.
15 Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi.
16 Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.
17 ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?
18 In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,
19 to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!
20 Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.
21 Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’