< Ayuba 39 >
1 “Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
“Have you known the time of The bearing of the wild goats of the rock? Do you mark the bringing forth of does?
2 Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa?
Do you number the months they fulfill? And have you known the time of their bringing forth?
3 Suna kwanciya su haifi’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.
They bow down, They bring forth their young ones safely, They cast forth their pangs.
4 ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa.
Their young ones are safe, They grow up in the field, they have gone out, And have not returned to them.
5 “Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi? Wane ne yake kunce igiyoyinsu?
Who has sent forth the wild donkey free? Indeed, who opened the bands of the wild donkey?
6 Na sa jeji yă zama gidansa ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.
Whose house I have made the wilderness, And his dwellings the barren land,
7 Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari; ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.
He laughs at the multitude of a city, He does not hear the cries of an exactor.
8 Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.
The range of mountains [is] his pasture, And he seeks after every green thing.
9 “Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
Is a wild ox willing to serve you? Does he lodge by your crib?
10 Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka?
Do you bind a wild ox in a furrow [with] his thick band? Does he harrow valleys after you?
11 Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka?
Do you trust in him because his power [is] great? And do you leave your labor to him?
12 Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka?
Do you trust in him That he brings back your seed, And gathers [it to] your threshing-floor?
13 “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
[The] wing of the crying ostriches exults, but as a pinion and feather of a stork?
14 Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
For she leaves her eggs on the earth, And she warms them on the dust,
15 ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
And she forgets that a foot may press it, And a beast of the field treads it down.
16 Tana tsananta wa’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
It has hardened her young ones without her, Her labor [is] in vain, without fear.
17 Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.
For God has caused her to forget wisdom, And He has not given a portion To her in understanding;
18 Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
At the time she lifts herself up on high, She laughs at the horse and his rider.
19 “Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
Do you give might to the horse? Do you clothe his neck [with] a mane?
20 Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
Do you cause him to rush as a locust? The splendor of his snorting [is] terrible.
21 Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
They dig in a valley, and he rejoices in power, He goes forth to meet the armor.
22 Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
He laughs at fear, and is not frightened, And he does not turn back from the face of the sword.
23 Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
Quiver rattles against him, The flame of a spear, and a javelin.
24 Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
He swallows the ground with trembling and rage, And does not remain steadfast Because of the sound of a horn.
25 Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi.
Among the horns he says, Aha, And from afar he smells battle, Roaring of princes and shouting.
26 “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?
By your understanding does a hawk fly? Does he spread his wings to the south?
27 Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama?
At your command does an eagle go up high? Or lift up his nest?
28 Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa.
He inhabits a rock, Indeed, he lodges on the tooth of a rock, and fortress.
29 Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa.
From there he has sought food, His eyes look attentively to a far-off place,
30 ’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”
And his brood sucks up blood, And where the pierced [are]—there [is] he!”