< Ayuba 38 >
1 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,
Then the Lord answered Job out of the whirlwind,
2 “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi?
“Who is this who questions my wisdom by talking so ignorantly?
3 Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini.
Prepare yourself, be strong, for I am going to question you, and you must answer me.
4 “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani.
Where were you when I laid the foundation of the earth? Tell me, if you have such knowledge!
5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?
Who decided its dimensions? Don't you know? Who stretched out a measuring line?
6 A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,
What do its foundations rest upon? Who laid its cornerstone,
7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.
when the stars of the morning sang together and all the angels shouted for joy.
8 “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.
Who laid down the boundaries of the sea when it was born?
9 Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,
Who clothed it with clouds, and wrapped it in a blanket of deep darkness?
10 sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa.
I set its limits, marking its borders.
11 Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?
I said, ‘You may come here, but no farther. Here is where your proud waves stop.’
12 “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito,
During your lifetime, have you ever ordered the morning to begin?
13 don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?
Have you ever told the dawn where to appear that it might take hold of the corners of the earth and shake the wicked out?
14 Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga.
The earth is changed like clay under a seal; its features stand out like a crumpled garment.
15 An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi.
The ‘light’ of the wicked is taken away from them; their acts of violence are stopped.
16 “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?
Have you entered the sources of the sea? Have you explored their hidden depths?
17 Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?
Have you been shown where the gates of death are? Have you seen the gates of utter darkness?
18 Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka.
Do you know how far the earth extends? Tell me if you know all this!
19 “Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama?
In which direction does light live? Where does darkness dwell?
20 Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?
Can you take them home? Do you know the way to where they live?
21 Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.
Of course you know, because you were already born then! You've lived so long!
22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara
Have you been to where the snow is kept? Have you seen where the hail is held?
23 waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa?
I have stored them up for the time of trouble, for the day of war and battle.
24 Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?
Do you know the way to where light comes from, or to where the east wind blows over the earth?
25 Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa
Who cuts a channel for the rain to flow? Who creates a path for the thunderbolt?
26 don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki
Who brings rain to an uninhabited land, to a desert where nobody lives,
27 don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can?
to water a parched wasteland to make the green grass grow?
28 Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa?
Does the rain have a father? Who was the father of the dewdrops?
29 Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai
Who was the mother of ice? Does the frost of the air have a mother?
30 lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare?
Water turns into rock-hard ice; its surface freezes solid.
31 “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?
Can you tie together the stars of the Pleiades? Can you loosen the belt of the Orion constellation?
32 Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da’ya’yanta zuwa waje?
Can you guide the stars of Mazzaroth at the right time? Can you direct the Great Bear constellation and its other stars?
33 Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?
Do you know the laws of the heavens? Can you apply them to the earth?
34 “Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?
Can you shout to the clouds and command them to pour rain down on you?
35 Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’
Can you send out bolts of lightning and direct them, so that they can answer you saying, ‘Here we are’?
36 Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa?
Who has placed wisdom inside people? Who has given understanding to the mind?
37 Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai
Who is clever enough to count the clouds? Who can turn heaven's water jars on their sides
38 sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya?
when the dust has baked into a solid mass?
39 “Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.
Can you hunt prey for the lion? Can you feed the lion cubs
40 Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?
as they crouch down in their dens and lie in wait in the bushes?
41 Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci?
Who provides food for the raven when its young cry out to God, weak from starvation?