< Ayuba 37 >

1 “Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.
אף-לזאת יחרד לבי ויתר ממקומו
2 Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa.
שמעו שמוע ברגז קלו והגה מפיו יצא
3 Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
תחת-כל-השמים ישרהו ואורו על-כנפות הארץ
4 Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu.
אחריו ישאג-קול-- ירעם בקול גאונו ולא יעקבם כי-ישמע קולו
5 Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
ירעם אל בקולו נפלאות עשה גדלות ולא נדע
6 Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
כי לשלג יאמר-- הוא-ארץ וגשם מטר וגשם מטרות עזו
7 Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
ביד-כל-אדם יחתום-- לדעת כל-אנשי מעשהו
8 Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu.
ותבוא חיה במו-ארב ובמעונתיה תשכן
9 Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.
מן-החדר תבוא סופה וממזרים קרה
10 Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
מנשמת-אל יתן-קרח ורחב מים במוצק
11 Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
אף-ברי יטריח עב יפיץ ענן אורו
12 Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi.
והוא מסבות מתהפך בתחבולתו לפעלם כל אשר יצום על-פני תבל ארצה
13 Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
אם-לשבט אם-לארצו-- אם-לחסד ימצאהו
14 “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
האזינה זאת איוב עמד והתבונן נפלאות אל
15 Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
התדע בשום-אלוה עליהם והפיע אור עננו
16 Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
התדע על-מפלשי-עב מפלאות תמים דעים
17 Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa,
אשר-בגדיך חמים-- בהשקט ארץ מדרום
18 ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi?
תרקיע עמו לשחקים חזקים כראי מוצק
19 “Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa; ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.
הודיענו מה-נאמר לו לא-נערך מפני-חשך
20 Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana? Ko wani zai nemi a haɗiye shi?
היספר-לו כי אדבר אם-אמר איש כי יבלע
21 Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta.
ועתה לא ראו אור-- בהיר הוא בשחקים ורוח עברה ותטהרם
22 Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya, Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.
מצפון זהב יאתה על-אלוה נורא הוד
23 Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu, shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci, ba ya cutar mutum.
שדי לא-מצאנהו שגיא-כח ומשפט ורב-צדקה לא יענה
24 Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”
לכן יראוהו אנשים לא-יראה כל-חכמי-לב

< Ayuba 37 >