< Ayuba 36 >
1 Elihu ya ci gaba,
2 “Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.
3 Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.
4 Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.
5 “Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.
6 Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.
7 Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.
8 Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,
9 yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.
10 Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu.
11 In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.
12 Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi.
13 “Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.
14 Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.
15 Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu.
16 “Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so.
17 Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye; shari’a da kuma gaskiya sun kama ka.
18 Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya.
19 Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?
20 Kada ka yi marmari dare yă yi, don a fitar da mutane daga gidajensu.
21 Ka kula kada ka juya ga mugunta, abin da ka fi so fiye da wahala.
22 “An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa?
23 Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’
24 Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
25 Dukan’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa.
26 Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27 “Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama.
28 Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa’yan adam a wadace.
29 Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
30 Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku.
31 Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace.
32 Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.
33 Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa.