< Ayuba 34 >

1 Sa’an nan Elihu ya ce,
ויען אליהוא ויאמר
2 “Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi.
שמעו חכמים מלי וידעים האזינו לי
3 Gama kunne yana rarrabe magana kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci.
כי-אזן מלין תבחן וחך יטעם לאכל
4 Bari mu zaɓi abin da yake daidai, bari mu koyi abin da yake mai kyau tare.
משפט נבחרה-לנו נדעה בינינו מה-טוב
5 “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.
כי-אמר איוב צדקתי ואל הסיר משפטי
6 Ko da yake ina da gaskiya, an ɗauke ni maƙaryaci; ko da yake ba ni da laifi, kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’
על-משפטי אכזב אנוש חצי בלי-פשע
7 Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa?
מי-גבר כאיוב ישתה-לעג כמים
8 Yana abokantaka da masu aikata mugunta; yana cuɗanya da mugaye.
וארח לחברה עם-פעלי און וללכת עם-אנשי-רשע
9 Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’
כי-אמר לא יסכן-גבר-- ברצתו עם-אלהים
10 “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure.
לכן אנשי לבב-- שמעו-לי חללה לאל מרשע ושדי מעול
11 Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.
כי פעל אדם ישלם-לו וכארח איש ימצאנו
12 Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.
אף-אמנם אל לא-ירשיע ושדי לא-יעות משפט
13 Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?
מי-פקד עליו ארצה ומי שם תבל כלה
14 In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,
אם-ישים אליו לבו רוחו ונשמתו אליו יאסף
15 ’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa.
יגוע כל-בשר יחד ואדם על-עפר ישוב
16 “In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce.
ואם-בינה שמעה-זאת האזינה לקול מלי
17 Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?
האף שונא משפט יחבוש ואם-צדיק כביר תרשיע
18 Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’
האמר למלך בליעל-- רשע אל-נדיבים
19 wanda ba ya nuna sonkai ga’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.
אשר לא-נשא פני שרים ולא נכר-שוע לפני-דל כי-מעשה ידיו כלם
20 Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.
רגע ימתו-- וחצות לילה יגעשו עם ויעברו ויסירו אביר לא ביד
21 “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.
כי-עיניו על-דרכי-איש וכל-צעדיו יראה
22 Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye.
אין-חשך ואין צלמות-- להסתר שם פעלי און
23 Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.
כי לא על-איש ישים עוד-- להלך אל-אל במשפט
24 Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu.
ירע כבירים לא-חקר ויעמד אחרים תחתם
25 Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.
לכן--יכיר מעבדיהם והפך לילה וידכאו
26 Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su,
תחת-רשעים ספקם-- במקום ראים
27 domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.
אשר על-כן סרו מאחריו וכל-דרכיו לא השכילו
28 Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.
להביא עליו צעקת-דל וצעקת עניים ישמע
29 Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,
והוא ישקט ומי ירשע-- ויסתר פנים ומי ישורנו ועל-גוי ועל-אדם יחד
30 yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko.
ממלך אדם חנף-- ממקשי עם
31 “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.
כי-אל-אל האמר נשאתי-- לא אחבל
32 Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’
בלעדי אחזה אתה הרני אם-עול פעלתי לא אסיף
33 Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani.
המעמך ישלמנה כי-מאסת--כי-אתה תבחר ולא-אני ומה-ידעת דבר
34 “Mutane masu ganewa za su ce, masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini,
אנשי לבב יאמרו לי וגבר חכם שמע לי
35 ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’
איוב לא-בדעת ידבר ודבריו לא בהשכיל
36 Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.
אבי--יבחן איוב עד-נצח על-תשבת באנשי-און
37 Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”
כי יסיף על-חטאתו פשע בינינו יספוק וירב אמריו לאל

< Ayuba 34 >