< Ayuba 33 >
1 “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.
“However, Job, please hear my speech, and listen to all my words.
2 Zan yi magana; kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.
See now, I have opened my mouth. My tongue has spoken in my mouth.
3 Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata; bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.
My words will utter the uprightness of my heart. That which my lips know they will speak sincerely.
4 Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.
The Spirit of God has made me, and the breath of the Almighty gives me life.
5 Ka amsa mini in za ka iya; ka yi shirin fuskanta ta.
If you can, answer me. Set your words in order before me, and stand up.
6 Ni kamar ka nake a gaban Allah; ni ma daga ƙasa aka yi ni.
Behold, I am toward God even as you are. I am also formed out of the clay.
7 Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka.
Behold, my terror will not make you afraid, neither will my pressure be heavy on you.
8 “Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa,
“Surely you have spoken in my hearing, I have heard the voice of your words, saying,
9 ‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi.
‘I am clean, without disobedience. I am innocent, neither is there iniquity in me.
10 Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa,
Behold, he finds occasions against me. He counts me for his enemy.
11 ya daure ƙafafuna da sarƙa; yana tsaron duk inda na bi.’
He puts my feet in the stocks. He marks all my paths.’
12 “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.
“Behold, I will answer you. In this you are not just, for God is greater than man.
13 Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?
Why do you strive against him, because he doesn’t give account of any of his matters?
14 Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.
For God speaks once, yes twice, though man pays no attention.
15 A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,
In a dream, in a vision of the night, when deep sleep falls on men, in slumbering on the bed,
16 mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,
then he opens the ears of men, and seals their instruction,
17 don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,
that he may withdraw man from his purpose, and hide pride from man.
18 don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.
He keeps back his soul from the pit, and his life from perishing by the sword.
19 “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,
“He is chastened also with pain on his bed, with continual strife in his bones,
20 yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.
so that his life abhors bread, and his soul dainty food.
21 Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.
His flesh is so consumed away that it can’t be seen. His bones that were not seen stick out.
22 Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da’yan aikan mutuwa.
Yes, his soul draws near to the pit, and his life to the destroyers.
23 Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,
“If there is beside him an angel, an interpreter, one among a thousand, to show to man what is right for him,
24 yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’
then God is gracious to him, and says, ‘Deliver him from going down to the pit, I have found a ransom.’
25 Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi.
His flesh will be fresher than a child’s. He returns to the days of his youth.
26 Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.
He prays to God, and he is favorable to him, so that he sees his face with joy. He restores to man his righteousness.
27 Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.
He sings before men, and says, ‘I have sinned, and perverted that which was right, and it didn’t profit me.
28 Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’
He has redeemed my soul from going into the pit. My life will see the light.’
29 “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.
“Behold, God does all these things, twice, yes three times, with a man,
30 Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.
to bring back his soul from the pit, that he may be enlightened with the light of the living.
31 “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana.
Mark well, Job, and listen to me. Hold your peace, and I will speak.
32 In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini; yi magana, domin ina so in’yantar da kai.
If you have anything to say, answer me. Speak, for I desire to justify you.
33 Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni; yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”
If not, listen to me. Hold your peace, and I will teach you wisdom.”