< Ayuba 32 >
1 Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.
2 Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.
3 Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.
4 Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.
5 Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.
6 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani.
7 Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’
8 Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.
9 Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.
10 “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani.
11 Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,
12 na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.
13 Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’
14 Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.
15 “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa; kalmomi sun kāsa musu.
16 Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.
17 Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani.
18 Gama ina cike da magana, kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;
19 a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.
20 Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa.
21 Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;
22 gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.