< Ayuba 31 >

1 “Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.
ברית כרתי לעיני ומה אתבונן על-בתולה
2 Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama, gādonsa daga Maɗaukaki a sama?
ומה חלק אלוה ממעל ונחלת שדי ממרמים
3 Ba masifa ba ne domin mugaye, hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?
הלא-איד לעול ונכר לפעלי און
4 Bai ga hanyoyina ba ne bai ƙirga kowace takawata ba?
הלא-הוא יראה דרכי וכל-צעדי יספור
5 “In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,
אם-הלכתי עם-שוא ותחש על-מרמה רגלי
6 Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya zai kuma san cewa ni marar laifi ne.
ישקלני במאזני-צדק וידע אלוה תמתי
7 In takawata ta kauce daga hanya, in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so, ko kuma in hannuwana suna da laifi;
אם תטה אשרי מני הדרך ואחר עיני הלך לבי ובכפי דבק מאום
8 bari waɗansu su ci abin da na shuka, kuma bari a tuge amfanin gonata.
אזרעה ואחר יאכל וצאצאי ישרשו
9 “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
אם-נפתה לבי על-אשה ועל-פתח רעי ארבתי
10 sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.
תטחן לאחר אשתי ועליה יכרעון אחרין
11 Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.
כי-הוא (היא) זמה והיא (והוא) עון פלילים
12 Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
כי אש היא עד-אבדון תאכל ובכל-תבואתי תשרש
13 “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,
אם-אמאס--משפט עבדי ואמתי ברבם עמדי
14 me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?
ומה אעשה כי-יקום אל וכי-יפקד מה אשיבנו
15 Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?
הלא-בבטן עשני עשהו ויכננו ברחם אחד
16 “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,
אם-אמנע מחפץ דלים ועיני אלמנה אכלה
17 in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,
ואכל פתי לבדי ולא-אכל יתום ממנה
18 amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.
כי מנעורי גדלני כאב ומבטן אמי אנחנה
19 In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,
אם-אראה אובד מבלי לבוש ואין כסות לאביון
20 kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,
אם-לא ברכוני חלצו ומגז כבשי יתחמם
21 in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,
אם-הניפותי על-יתום ידי כי-אראה בשער עזרתי
22 bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.
כתפי משכמה תפול ואזרעי מקנה תשבר
23 Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.
כי פחד אלי איד אל ומשאתו לא אוכל
24 “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’
אם-שמתי זהב כסלי ולכתם אמרתי מבטחי
25 in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.
אם-אשמח כי-רב חילי וכי-כביר מצאה ידי
26 In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa,
אם-אראה אור כי יהל וירח יקר הלך
27 zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su.
ויפת בסתר לבי ותשק ידי לפי
28 Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
גם-הוא עון פלילי כי-כחשתי לאל ממעל
29 “In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi,
אם-אשמח בפיד משנאי והתעררתי כי-מצאו רע
30 ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba,
ולא-נתתי לחטא חכי-- לשאל באלה נפשו
31 in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’
אם-לא אמרו מתי אהלי מי-יתן מבשרו לא נשבע
32 Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,
בחוץ לא-ילין גר דלתי לארח אפתח
33 in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,
אם-כסיתי כאדם פשעי-- לטמון בחבי עוני
34 domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.
כי אערוץ המון רבה-- ובוז-משפחות יחתני ואדם לא-אצא פתח
35 (“Kash, da ina da wanda zai ji ni! Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina, bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.
מי יתן-לי שמע לי-- הן-תוי שדי יענני וספר כתב איש ריבי
36 Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata, zan aza a kaina kamar rawani.
אם-לא על-שכמי אשאנו אענדנו עטרות לי
37 Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi; zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)
מספר צעדי אגידנו כמו-נגיד אקרבנו
38 “In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye,
אם-עלי אדמתי תזעק ויחד תלמיה יבכיון
39 in na kwashe amfaninta ban biya ba ko kuma na kashe masu ita,
אם-כחה אכלתי בלי-כסף ונפש בעליה הפחתי
40 bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.
תחת חטה יצא חוח--ותחת-שערה באשה תמו דברי איוב

< Ayuba 31 >