< Ayuba 3 >
1 Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi.
2 Ayuba ya ce,
3 “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’
4 Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana.
5 Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta.
6 Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni.
7 Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki.
8 Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa.
9 Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani,
10 gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba.
11 “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?
12 Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu?
13 Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama
14 tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,
15 da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.
16 Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.
17 A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta.
18 Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.
19 Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami’yanci daga wurin maigidansa.
20 “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai
21 ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye,
22 waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari?
23 Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi.
24 Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa;
25 Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni.
26 Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.”