< Ayuba 29 >
1 Ayuba ya ci gaba da jawabinsa,
And Job again took up his parable, and said:
2 “Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can, kwanakin da Allah yake lura da ni,
Oh that I were as in the months of old, as in the days when God watched over me;
3 lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.
When His lamp shined above my head, and by His light I walked through darkness;
4 Kwanakin da nake tasowa, lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,
As I was in the days of my youth, when the converse of God was upon my tent;
5 lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni, kuma’ya’yana suna kewaye da ni,
When the Almighty was yet with me, and my children were about me;
6 lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa, duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.
When my steps were washed with butter, and the rock poured me out rivers of oil!
7 “Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna a bainin jama’a,
When I went forth to the gate unto the city, when I prepared my seat in the broad place,
8 matasan da suka gan ni sukan ja gefe tsofaffi kuma suka tashi tsaye;
The young men saw me and hid themselves, and the aged rose up and stood;
9 sarakuna suka yi shiru suka rufe bakunansu da hannuwansu;
The princes refrained talking, and laid their hand on their mouth;
10 Muryar manya ta yi tsit harshensu ya manne a rufin bakunansu.
The voice of the nobles was hushed, and their tongue cleaved to the roof of their mouth.
11 Duk wanda ya ji ni ya yaba mini waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,
For when the ear heard me, then it blessed me, and when the eye saw me, it gave witness unto me;
12 domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
Because I delivered the poor that cried, the fatherless also, that had none to help him.
13 Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya.
The blessing of him that was ready to perish came upon me; and I caused the widow's heart to sing for joy.
14 Na yafa adalci ya zama suturata; gaskiya ita ce rigata da rawanina.
I put on righteousness, and it clothed itself with me; my justice was as a robe and a diadem.
15 Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu.
I was eyes to the blind, and feet was I to the lame.
16 Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo.
I was a father to the needy; and the cause of him that I knew not I searched out.
17 Na karya ƙarfin mugaye na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.
And I broke the jaws of the unrighteous, and plucked the prey out of his teeth.
18 “Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana, kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.
Then I said: 'I shall die with my nest, and I shall multiply my days as the phoenix;
19 Jijiyoyina za su kai cikin ruwa, kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.
My root shall be spread out to the waters, and the dew shall lie all night upon my branch;
20 Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau, bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’
My glory shall be fresh in me, and my bow shall be renewed in my hand.'
21 “Mutane suna mai da hankali su saurare ni, suna yin shiru don su ji shawarata.
Unto me men gave ear, and waited, and kept silence for my counsel.
22 Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba. Maganata ta shige su.
After my words they spoke not again; and my speech dropped upon them.
23 Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama. Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.
And they waited for me as for the rain; and they opened their mouth wide as for the latter rain.
24 Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda; hasken fuskata yana da daraja a gare su.
If I laughed on them, they believed it not; and the light of my countenance they cast not down.
25 Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin rundunansu; ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.
I chose out their way, and sat as chief, and dwelt as a king in the army, as one that comforteth the mourners.