< Ayuba 28 >
1 Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya.
2 Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.
3 Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.
4 Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi.
5 Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;
6 akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.
7 Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba, ba shahon da ya taɓa ganin ta.
8 Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta.
9 Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.
10 Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.
11 Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.
12 Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama?
13 Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai.
14 Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.”
15 Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.
16 Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.
17 Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.
18 Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.
19 Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.
20 “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?
21 An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.
22 Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’
23 Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,
24 Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.
25 Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.
26 Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,
27 sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.
28 Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’”