< Ayuba 27 >
1 Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,
2 “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
3 Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
4 bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
5 Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
6 Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.
7 “Bari maƙiyana su zama kamar mugaye, masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci.
8 Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?
9 Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?
10 Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
11 “Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.
12 Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?
13 “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.
14 Kome yawan’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.
15 Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.
16 Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa,
17 abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa.
18 Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.
19 Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.
20 Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.
21 Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa.
22 Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.
23 Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.”