< Ayuba 26 >

1 Sai Ayuba ya amsa,
約伯回答說:
2 “Yadda ka taimaki marar ƙarfi! Yadda ka ceci marar ƙarfi!
無能的人蒙你何等的幫助! 膀臂無力的人蒙你何等的拯救!
3 Ka ba marar hikima shawara! Ka nuna kana da ilimi sosai.
無智慧的人蒙你何等的指教! 你向他多顯大知識!
4 Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu? Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?
你向誰發出言語來? 誰的靈從你而出?
5 “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukan mazauna cikin ruwaye.
在大水和水族以下的陰魂戰兢。
6 Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe. (Sheol h7585)
在上帝面前,陰間顯露; 滅亡也不得遮掩。 (Sheol h7585)
7 Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
上帝將北極鋪在空中, 將大地懸在虛空;
8 Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
將水包在密雲中, 雲卻不破裂;
9 Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
遮蔽他的寶座, 將雲鋪在其上;
10 ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
在水面的周圍劃出界限, 直到光明黑暗的交界。
11 Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.
天的柱子因他的斥責震動驚奇。
12 Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
他以能力攪動大海; 他藉知識打傷拉哈伯,
13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
藉他的靈使天有妝飾; 他的手刺殺快蛇。
14 Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”
看哪,這不過是上帝工作的些微; 我們所聽於他的是何等細微的聲音! 他大能的雷聲誰能明透呢?

< Ayuba 26 >