< Ayuba 25 >

1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, 2 “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama. 3 Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa? 4 Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki? 5 In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa, 6 mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”

< Ayuba 25 >