< Ayuba 24 >
1 “Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba? Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan?
Why are not times treasured up by the Almighty? And why do not they who know him see his days?
2 Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.
They remove landmarks; They take away flocks by violence, and pasture them.
3 Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.
They drive away the ass of the fatherless, And take the widow's ox for a pledge.
4 Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.
They push the needy from the way; All the poor of the land are forced to hide themselves.
5 Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa’ya’yansu.
Behold, like wild asses of the desert, they go forth to their work; They search for prey; The wilderness supplieth them food for their children.
6 Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.
In the fields they reap the harvest, And gather the vintage of the oppressor.
7 Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.
They lodge naked, without clothing, And without covering from the cold.
8 Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.
They are drenched with the mountain showers, And embrace the rock for want of shelter.
9 Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.
The fatherless are torn from the breast, And the garment of the needy is taken for a pledge.
10 Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.
They go naked, without clothing, And carry the sheaf hungry.
11 Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.
They make oil within their walls, And tread the wine-vat, yet suffer thirst.
12 Ana jin nishin masu mutuwa daga birni, kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako. Amma bai ba wani laifi ba.
From anguish the dying groan, And the wounded cry aloud; And God regardeth not their prayer!
13 “Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye, waɗanda ba su san hanyoyinsa ba ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba.
Others hate the light; They know not its ways, And abide not in its paths.
14 Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi; yă je yă kashe matalauta da masu bukata; a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.
With the light ariseth the murderer; He killeth the poor and needy; In the night he is as a thief.
15 Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai; yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’ sai kuma yă ɓoye fuskarsa.
The eye of the adulterer watcheth for the twilight; He saith, “No eye will see me,” And putteth a mask upon his face.
16 Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.
In the dark they break into houses; In the daytime they shut themselves up; They are strangers to the light.
17 Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu; suna abokantaka da razanar duhu.
The morning is to them the very shadow of death; They are familiar with the terrors of the shadow of death.
18 “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.
Light are they on the face of the waters; They have an accursed portion in the earth; They come not near the vineyards.
19 Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke, haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi. (Sheol )
As drought and heat consume the snow waters, So doth the grave the wicked. (Sheol )
20 Waɗanda suka haife su za su manta da su, tsutsotsi za su cinye su; ba za a sāke tunawa da mugaye ba amma an sare su kamar itace.
His own mother forgetteth him; The worm feedeth sweetly on him; He is no more remembered, And iniquity is broken like a tree.
21 Suna cutar macen da ba ta da ɗa, suna nuna wa gwauruwa rashin alheri.
He oppresseth the barren, that hath not borne, And doeth not good to the widow.
22 Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi, ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa.
He taketh away the mighty by his power; He riseth up, and no one is sure of life.
23 Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali, amma idanunsa suna kansu.
God giveth them security, so that they are confident; His eyes are upon their ways.
24 Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci, amma kuma za su ɓace; za su fāɗi a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi.
They are exalted; —in a little while they are gone! They are brought low, and die, like all others; And like the topmost ears of corn are they cut off.
25 “In wannan ba haka ba ne, wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?”
If it be not so, who will confute me, And show my discourse to be worthless?