< Ayuba 22 >

1 Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
וַ֭יַּעַן אֱלִיפַ֥ז הַֽתֵּמָנִ֗י וַיֹּאמַֽר׃
2 “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?
הַלְאֵ֥ל יִסְכָּן־גָּ֑בֶר כִּֽי־יִסְכֹּ֖ן עָלֵ֣ימוֹ מַשְׂכִּֽיל׃
3 Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?
הַחֵ֣פֶץ לְ֭שַׁדַּי כִּ֣י תִצְדָּ֑ק וְאִם־בֶּ֝֗צַע כִּֽי־תַתֵּ֥ם דְּרָכֶֽיךָ׃
4 “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka?
הֲֽ֭מִיִּרְאָ֣תְךָ יֹכִיחֶ֑ךָ יָב֥וֹא עִ֝מְּךָ֗ בַּמִּשְׁפָּֽט׃
5 Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba?
הֲלֹ֣א רָעָֽתְךָ֣ רַבָּ֑ה וְאֵֽין־קֵ֝֗ץ לַעֲוֹנֹתֶֽיךָ׃
6 Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
כִּֽי־תַחְבֹּ֣ל אַחֶ֣יךָ חִנָּ֑ם וּבִגְדֵ֖י עֲרוּמִּ֣ים תַּפְשִֽׁיט׃
7 Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.
לֹא־מַ֭יִם עָיֵ֣ף תַּשְׁקֶ֑ה וּ֝מֵרָעֵ֗ב תִּֽמְנַֽע־לָֽחֶם׃
8 Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
וְאִ֣ישׁ זְ֭רוֹעַ ל֣וֹ הָאָ֑רֶץ וּנְשׂ֥וּא פָ֝נִ֗ים יֵ֣שֶׁב בָּֽהּ׃
9 Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu.
אַ֭לְמָנוֹת שִׁלַּ֣חְתָּ רֵיקָ֑ם וּזְרֹע֖וֹת יְתֹמִ֣ים יְדֻכָּֽא׃
10 Shi ya sa kake kewaye da tarkuna, shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.
עַל־כֵּ֭ן סְבִיבוֹתֶ֣יךָ פַחִ֑ים וִֽ֝יבַהֶלְךָ פַּ֣חַד פִּתְאֹֽם׃
11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
אוֹ־חֹ֥שֶׁךְ לֹֽא־תִרְאֶ֑ה וְֽשִׁפְעַת־מַ֥יִם תְּכַסֶּֽךָּ׃
12 “Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
הֲֽלֹא־אֱ֭לוֹהַּ גֹּ֣בַהּ שָׁמָ֑יִם וּרְאֵ֤ה רֹ֖אשׁ כּוֹכָבִ֣ים כִּי־רָֽמּוּ׃
13 Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a?
וְֽ֭אָמַרְתָּ מַה־יָּ֣דַֽע אֵ֑ל הַבְעַ֖ד עֲרָפֶ֣ל יִשְׁפּֽוֹט׃
14 Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’
עָבִ֣ים סֵֽתֶר־ל֭וֹ וְלֹ֣א יִרְאֶ֑ה וְח֥וּג שָׁ֝מַ֗יִם יִתְהַלָּֽךְ׃
15 Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar da mugayen mutane suka bi?
הַאֹ֣רַח עוֹלָ֣ם תִּשְׁמֹ֑ר אֲשֶׁ֖ר דָּרְכ֣וּ מְתֵי־אָֽוֶן׃
16 An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika, ruwa ya share tushensu.
אֲשֶֽׁר־קֻמְּט֥וּ וְלֹא־עֵ֑ת נָ֝הָ֗ר יוּצַ֥ק יְסוֹדָֽם׃
17 Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’
הָאֹמְרִ֣ים לָ֭אֵל ס֣וּר מִמֶּ֑נּוּ וּמַה־יִּפְעַ֖ל שַׁדַּ֣י לָֽמוֹ׃
18 Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
וְה֤וּא מִלֵּ֣א בָתֵּיהֶ֣ם ט֑וֹב וַעֲצַ֥ת רְ֝שָׁעִ֗ים רָ֣חֲקָה מֶֽנִּי׃
19 “Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi; marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,
יִרְא֣וּ צַדִּיקִ֣ים וְיִשְׂמָ֑חוּ וְ֝נָקִ֗י יִלְעַג־לָֽמוֹ׃
20 ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
אִם־לֹ֣א נִכְחַ֣ד קִימָ֑נוּ וְ֝יִתְרָ֗ם אָ֣כְלָה אֵֽשׁ׃
21 “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka.
הַסְכֶּן־נָ֣א עִמּ֑וֹ וּשְׁלם בָּ֝הֶ֗ם תְּֽבוֹאַתְךָ֥ טוֹבָֽה׃
22 Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.
קַח־נָ֣א מִפִּ֣יו תּוֹרָ֑ה וְשִׂ֥ים אֲ֝מָרָ֗יו בִּלְבָבֶֽךָ׃
23 In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
אִם־תָּשׁ֣וּב עַד־שַׁ֭דַּי תִּבָּנֶ֑ה תַּרְחִ֥יק עַ֝וְלָ֗ה מֵאָהֳלֶֽךָ׃
24 Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
וְשִׁית־עַל־עָפָ֥ר בָּ֑צֶר וּבְצ֖וּר נְחָלִ֣ים אוֹפִֽיר׃
25 sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
וְהָיָ֣ה שַׁדַּ֣י בְּצָרֶ֑יךָ וְכֶ֖סֶף תּוֹעָפ֣וֹת לָֽךְ׃
26 Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
כִּי־אָ֭ז עַל־שַׁדַּ֣י תִּתְעַנָּ֑ג וְתִשָּׂ֖א אֶל־אֱל֣וֹהַּ פָּנֶֽיךָ׃
27 Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.
תַּעְתִּ֣יר אֵ֭לָיו וְיִשְׁמָעֶ֑ךָּ וּנְדָרֶ֥יךָ תְשַׁלֵּֽם׃
28 Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka.
וְֽתִגְזַר־א֭וֹמֶר וְיָ֣קָם לָ֑ךְ וְעַל־דְּ֝רָכֶ֗יךָ נָ֣גַֽהּ אֽוֹר׃
29 Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.
כִּֽי־הִ֭שְׁפִּילוּ וַתֹּ֣אמֶר גֵּוָ֑ה וְשַׁ֖ח עֵינַ֣יִם יוֹשִֽׁעַ׃
30 Zai ceci wanda ma yake mai laifi, wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”
יְֽמַלֵּ֥ט אִֽי־נָקִ֑י וְ֝נִמְלַ֗ט בְּבֹ֣ר כַּפֶּֽיךָ׃ פ

< Ayuba 22 >