< Ayuba 21 >

1 Sai Ayuba ya amsa,
וַיַּעַן אִיּוֹב וַיֹּאמַֽר׃
2 “Ku saurare ni da kyau; bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.
שִׁמְעוּ שָׁמוֹעַ מִלָּתִי וּתְהִי־זֹאת תַּנְחוּמֹֽתֵיכֶֽם׃
3 Ku ba ni zarafi in yi magana, bayan na gama sai ku yi ba’arku.
שָׂאוּנִי וְאָנֹכִי אֲדַבֵּר וְאַחַר דַּבְּרִי תַלְעִֽיג׃
4 “A wurin mutum ne na kawo kukana? Don me ba zan kāsa haƙuri ba?
הֶאָנֹכִי לְאָדָם שִׂיחִי וְאִם־מַדּוּעַ לֹֽא־תִקְצַר רוּחִֽי׃
5 Ku dube ni, ku kuma yi mamaki; ku rufe bakina da hannunku.
פְּנוּ־אֵלַי וְהָשַׁמּוּ וְשִׂימוּ יָד עַל־פֶּֽה׃
6 Lokacin da na yi tunanin wannan, sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.
וְאִם־זָכַרְתִּי וְנִבְהָלְתִּי וְאָחַז בְּשָׂרִי פַּלָּצֽוּת׃
7 Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa, suna kuma ƙaruwa da iko?
מַדּוּעַ רְשָׁעִים יִֽחְיוּ עָתְקוּ גַּם־גָּבְרוּ חָֽיִל׃
8 Suna ganin’ya’yansu suna girma, suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.
זַרְעָם נָכוֹן לִפְנֵיהֶם עִמָּם וְצֶאֱצָאֵיהֶם לְעֵינֵיהֶֽם׃
9 Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo.
בָּתֵּיהֶם שָׁלוֹם מִפָּחַד וְלֹא שֵׁבֶט אֱלוֹהַּ עֲלֵיהֶֽם׃
10 Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari.
שׁוֹרוֹ עִבַּר וְלֹא יַגְעִל תְּפַלֵּט פָּרָתוֹ וְלֹא תְשַׁכֵּֽל׃
11 Suna aika’ya’yansu kamar garke;’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.
יְשַׁלְּחוּ כַצֹּאן עֲוִילֵיהֶם וְיַלְדֵיהֶם יְרַקֵּדֽוּן׃
12 Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.
יִשְׂאוּ כְּתֹף וְכִנּוֹר וְיִשְׂמְחוּ לְקוֹל עוּגָֽב׃
13 Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama. (Sheol h7585)
(יבלו) [יְכַלּוּ] בַטּוֹב יְמֵיהֶם וּבְרֶגַע שְׁאוֹל יֵחָֽתּוּ׃ (Sheol h7585)
14 Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.
וַיֹּאמְרוּ לָאֵל סוּר מִמֶּנּוּ וְדַעַת דְּרָכֶיךָ לֹא חָפָֽצְנוּ׃
15 Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?
מַה־שַּׁדַּי כִּֽי־נַעַבְדֶנּוּ וּמַה־נּוֹעִיל כִּי נִפְגַּע־בּֽוֹ׃
16 Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
הֵן לֹא בְיָדָם טוּבָם עֲצַת רְשָׁעִים רָחֲקָה מֶֽנִּי׃
17 “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?
כַּמָּה ׀ נֵר־רְשָׁעִים יִדְעָךְ וְיָבֹא עָלֵימוֹ אֵידָם חֲבָלִים יְחַלֵּק בְּאַפּֽוֹ׃
18 Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska, ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?
יִֽהְיוּ כְּתֶבֶן לִפְנֵי־רוּחַ וּכְמֹץ גְּנָבַתּוּ סוּפָֽה׃
19 An ce ‘Allah yana tara wa’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!
אֱלוֹהַּ יִצְפֹּן־לְבָנָיו אוֹנוֹ יְשַׁלֵּם אֵלָיו וְיֵדָֽע׃
20 Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka; bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.
יִרְאוּ עֵינָו כִּידוֹ וּמֵחֲמַת שַׁדַּי יִשְׁתֶּֽה׃
21 Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?
כִּי מַה־חֶפְצוֹ בְּבֵיתוֹ אַחֲרָיו וּמִסְפַּר חֳדָשָׁיו חֻצָּֽצוּ׃
22 “Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?
הַלְאֵל יְלַמֶּד־דָּעַת וְהוּא רָמִים יִשְׁפּֽוֹט׃
23 Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,
זֶה יָמוּת בְּעֶצֶם תֻּמּוֹ כֻּלּוֹ שַׁלְאֲנַן וְשָׁלֵֽיו׃
24 jikinsa ɓulɓul, ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.
עֲטִינָיו מָלְאוּ חָלָב וּמֹחַ עַצְמוֹתָיו יְשֻׁקֶּֽה׃
25 Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai, bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.
וְזֶה יָמוּת בְּנֶפֶשׁ מָרָה וְלֹֽא־אָכַל בַּטּוֹבָֽה׃
26 Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa, kuma tsutsotsi za su cinye su.
יַחַד עַל־עָפָר יִשְׁכָּבוּ וְרִמָּה תְּכַסֶּה עֲלֵיהֶֽם׃
27 “Na san duk abin da kuke tunani, yadda za ku saɓa mini.
הֵן יָדַעְתִּי מַחְשְׁבֽוֹתֵיכֶם וּמְזִמּוֹת עָלַי תַּחְמֹֽסוּ׃
28 Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan, tenti wurin da mugaye suke zama?’
כִּי תֹאמְרוּ אַיֵּה בֵית־נָדִיב וְאַיֵּה אֹהֶל ׀ מִשְׁכְּנוֹת רְשָׁעִֽים׃
29 Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba? Ba ku kula da labaransu,
הֲלֹא שְׁאֶלְתֶּם עוֹבְרֵי דָרֶךְ וְאֹתֹתָם לֹא תְנַכֵּֽרוּ׃
30 cewa an kāre mugu daga ranar bala’i, an kāre shi daga ranar fushi?
כִּי לְיוֹם אֵיד יֵחָשֶׂךְ רָע לְיוֹם עֲבָרוֹת יוּבָֽלוּ׃
31 Wane ne yake gaya masa abin da ya yi? Wane ne yake rama abin da ya yi?
מִֽי־יַגִּיד עַל־פָּנָיו דַּרְכּוֹ וְהוּא־עָשָׂה מִי יְשַׁלֶּם־לֽוֹ׃
32 Za a bizne shi a kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa.
וְהוּא לִקְבָרוֹת יוּבָל וְֽעַל־גָּדִישׁ יִשְׁקֽוֹד׃
33 Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali; dukan jama’a suna binsa, da yawa kuma suna gabansa.
מָֽתְקוּ־לוֹ רִגְבֵי ־ נָחַל וְאַחֲרָיו כׇּל־אָדָם יִמְשׁוֹךְ וּלְפָנָיו אֵין מִסְפָּֽר׃
34 “Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”
וְאֵיךְ תְּנַחֲמוּנִי הָבֶל וּתְשׁוּבֹתֵיכֶם נִשְׁאַר־מָֽעַל׃

< Ayuba 21 >