< Ayuba 20 >
1 Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
2 “Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa domin abin ya dame ni sosai.
3 Na ji wani zargin da ka yi mini na reni, kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.
4 “Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya,
5 mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.
6 Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama, kansa kuma yana taɓa gizagizai.
7 Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa; waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’
8 Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba zai ɓace kamar wahayi da dare.
9 Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba; wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.
10 Dole’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.
11 Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura.
12 “Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa,
13 ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa,
14 duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.
15 Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.
16 Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.
17 Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.
18 Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.
19 Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.
20 “Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba.
21 Ba abin da ya ragu da zai ɗauka; arzikinsa ba zai dawwama ba.
22 Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa; ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.
23 Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi.
24 Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe, kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.
25 Zai zāre ta daga bayansa, tsinin zai fita daga hantarsa; tsoro zai cika shi;
26 duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.
27 Sammai za su fallasa laifinsa; duniya za tă yi gāba da shi.
28 Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.
29 Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.”