< Ayuba 2 >
1 Wata rana kuma mala’iku suka sāke kawo kansu gaban Ubangiji, sai Shaiɗan shi ma ya zo tare da su yă nuna kansa a gabansa.
2 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
3 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”
4 Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa.
5 Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.”
6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”
7 Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa.
8 Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.
9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
10 Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
11 Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi.
12 Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu,
13 sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.