< Ayuba 19 >

1 Sai Ayuba ya amsa,
וַיַּעַן אִיּוֹב וַיֹּאמַֽר׃
2 “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku?
עַד־אָנָה תּוֹגְיוּן נַפְשִׁי וּֽתְדַכְּאוּנַנִי בְמִלִּֽים׃
3 Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni, kuna kai mini hari na rashin kunya.
זֶה עֶשֶׂר פְּעָמִים תַּכְלִימוּנִי לֹֽא־תֵבֹשׁוּ תַּהְכְּרוּ־לִֽי׃
4 In gaskiya ne na yi laifi, kuskurena ya rage nawa.
וְאַף־אָמְנָם שָׁגִיתִי אִתִּי תָּלִין מְשׁוּגָתִֽי׃
5 In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,
אִם־אָמְנָם עָלַי תַּגְדִּילוּ וְתוֹכִיחוּ עָלַי חֶרְפָּתִּֽי׃
6 sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.
דְּֽעוּ־אֵפוֹ כִּי־אֱלוֹהַּ עִוְּתָנִי וּמְצוּדוֹ עָלַי הִקִּֽיף׃
7 “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.
הֵן אֶצְעַק חָמָס וְלֹא אֵעָנֶה אֲשַׁוַּע וְאֵין מִשְׁפָּֽט׃
8 Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba; ya rufe hanyata da duhu.
אָרְחִי גָדַר וְלֹא אֶעֱבוֹר וְעַל נְתִיבוֹתַי חֹשֶׁךְ יָשִֽׂים׃
9 Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina.
כְּבוֹדִי מֵעָלַי הִפְשִׁיט וַיָּסַר עֲטֶרֶת רֹאשִֽׁי׃
10 Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare; ya tuge begen da nake da shi kamar itace.
יִתְּצֵנִי סָבִיב וָאֵלַךְ וַיַּסַּע כָּעֵץ תִּקְוָתִֽי׃
11 Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa.
וַיַּחַר עָלַי אַפּוֹ וַיַּחְשְׁבֵנִי לוֹ כְצָרָֽיו׃
12 Rundunarsa ta zo da ƙarfi; suka kafa sansani kewaye da ni, suka zagaye tentina.
יַחַד ׀ יָבֹאוּ גְדוּדָיו וַיָּסֹלּוּ עָלַי דַּרְכָּם וַיַּחֲנוּ סָבִיב לְאָהֳלִֽי׃
13 “Ya raba ni da’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni.
אַחַי מֵעָלַי הִרְחִיק וְיֹדְעַי אַךְ־זָרוּ מִמֶּֽנִּי׃
14 Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni.
חָדְלוּ קְרוֹבָי וּֽמְיֻדָּעַי שְׁכֵחֽוּנִי׃
15 Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.
גָּרֵי בֵיתִי וְאַמְהֹתַי לְזָר תַּחְשְׁבֻנִי נָכְרִי הָיִיתִי בְעֵינֵיהֶֽם׃
16 Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.
לְעַבְדִּי קָרָאתִי וְלֹא יַעֲנֶה בְּמוֹ־פִי אֶתְחַנֶּן־לֽוֹ׃
17 Numfashina yana ɓata wa matata rai;’yan’uwana sun ƙi ni.
רוּחִֽי זָרָה לְאִשְׁתִּי וְחַנֹּתִי לִבְנֵי בִטְנִֽי׃
18 Har’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.
גַּם־עֲוִילִים מָאֲסוּ בִי אָקוּמָה וַיְדַבְּרוּ־בִֽי׃
19 Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
תִּֽעֲבוּנִי כָּל־מְתֵי סוֹדִי וְזֶֽה־אָהַבְתִּי נֶהְפְּכוּ־בִֽי׃
20 Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira.
בְּעוֹרִי וּבִבְשָׂרִי דָּבְקָה עַצְמִי וָאֶתְמַלְּטָה בְּעוֹר שִׁנָּֽי׃
21 “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.
חָנֻּנִי חָנֻּנִי אַתֶּם רֵעָי כִּי יַד־אֱלוֹהַּ נָגְעָה בִּֽי׃
22 Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba?
לָמָּה תִּרְדְּפֻנִי כְמוֹ־אֵל וּמִבְּשָׂרִי לֹא תִשְׂבָּֽעוּ׃
23 “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi,
מִֽי־יִתֵּן אֵפוֹ וְיִכָּתְבוּן מִלָּי מִֽי־יִתֵּן בַּסֵּפֶר וְיֻחָֽקוּ׃
24 a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada!
בְּעֵט־בַּרְזֶל וְעֹפָרֶת לָעַד בַּצּוּר יֵחָצְבֽוּן׃
25 Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.
וַאֲנִי יָדַעְתִּי גֹּאֲלִי חָי וְאַחֲרוֹן עַל־עָפָר יָקֽוּם׃
26 Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.
וְאַחַר עוֹרִֽי נִקְּפוּ־זֹאת וּמִבְּשָׂרִי אֶֽחֱזֶה אֱלֽוֹהַּ׃
27 Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!
אֲשֶׁר אֲנִי ׀ אֶֽחֱזֶה־לִּי וְעֵינַי רָאוּ וְלֹא־זָר כָּלוּ כִלְיֹתַי בְּחֵקִֽי׃
28 “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini, tun da shi ne tushen damuwa,’
כִּי תֹאמְרוּ מַה־נִּרְדָּף־לוֹ וְשֹׁרֶשׁ דָּבָר נִמְצָא־בִֽי׃
29 sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”
גּוּרוּ לָכֶם ׀ מִפְּנֵי־חֶרֶב כִּֽי־חֵמָה עֲוֺנוֹת חָרֶב לְמַעַן תֵּדְעוּן שדין שַׁדּֽוּן׃

< Ayuba 19 >