< Ayuba 18 >
1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
Then Bildad the Shuhite replied:
2 “Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.
“How long until you end these speeches? Show some sense, and then we can talk.
3 Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi?
Why are we regarded as cattle, as stupid in your sight?
4 Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?
You who tear yourself in anger— should the earth be forsaken on your account, or the rocks be moved from their place?
5 “An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci.
Indeed, the lamp of the wicked is extinguished; the flame of his fire does not glow.
6 Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu.
The light in his tent grows dark, and the lamp beside him goes out.
7 Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa.
His vigorous stride is shortened, and his own schemes trip him up.
8 Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.
For his own feet lead him into a net, and he wanders into its mesh.
9 Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam.
A trap seizes his heel; a snare grips him.
10 An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
A noose is hidden in the ground, and a trap lies in his path.
11 Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je.
Terrors frighten him on every side and harass his every step.
12 Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.
His strength is depleted, and calamity is ready at his side.
13 Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.
It devours patches of his skin; the firstborn of death devours his limbs.
14 An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai.
He is torn from the shelter of his tent and is marched off to the king of terrors.
15 Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama.
Fire resides in his tent; burning sulfur rains down on his dwelling.
16 Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama.
The roots beneath him dry up, and the branches above him wither away.
17 An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
The memory of him perishes from the earth, and he has no name in the land.
18 An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya.
He is driven from light into darkness and is chased from the inhabited world.
19 Ba shi da’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.
He has no offspring or posterity among his people, no survivor where he once lived.
20 Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas.
Those in the west are appalled at his fate, while those in the east tremble in horror.
21 Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”
Surely such is the dwelling of the wicked and the place of one who does not know God.”