< Ayuba 17 >

1 Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana.
Mon souffle se perd; mes jours s'éteignent; le tombeau m'attend!
2 Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
Certes, je suis entouré de railleurs, et mon œil veille toute la nuit au milieu de leurs insultes.
3 “Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari. Wane ne zai kāre ni?
Dépose un gage, sois ma caution auprès de toi-même; car qui voudrait répondre pour moi?
4 Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
Tu as fermé leur cœur à l'intelligence; c'est pourquoi tu ne les feras pas triompher.
5 In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada’ya’yansa za su makance.
Tel livre ses amis au pillage, dont les enfants auront les yeux consumés.
6 “Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.
On a fait de moi la fable des peuples, un être à qui l'on crache au visage.
7 Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki; jikina ya zama kamar inuwa kawai
Et mon œil s'est consumé de chagrin, et tous mes membres sont comme une ombre.
8 Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro; marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.
Les hommes droits en sont consternés, et l'innocent est irrité contre l'impie.
9 Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.
Le juste néanmoins persévère dans sa voie, et celui dont les mains sont pures redouble de constance.
10 “Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa! Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.
Mais, pour vous tous, allons, recommencez! Je ne trouverai pas un sage parmi vous.
11 Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so.
Mes jours sont passés; mes desseins, chers à mon cœur, sont renversés.
12 Mutanen nan sun juya rana ta zama dare. A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’
Ils changent la nuit en jour; ils disent la lumière proche, en face des ténèbres!
13 In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu, (Sheol h7585)
Quand je n'attends plus pour demeure que le Sépulcre, quand j'étends ma couche dans les ténèbres, (Sheol h7585)
14 In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
Quand je crie au tombeau: Tu es mon père! et aux vers: Vous êtes ma mère et ma sœur!
15 To, ina begena yake? Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
Où est donc mon espérance? Et mon espérance, qui pourrait la voir?
16 Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?” (Sheol h7585)
Elle descendra aux portes du Sépulcre, quand nous irons en-semble reposer dans la poussière! (Sheol h7585)

< Ayuba 17 >