< Ayuba 15 >
1 Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
2 “Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado ko yă cika cikinsa da iskar gabas?
3 Ko zai yi gardama da maganganun wofi maganganu marasa amfani?
4 Amma ka ma rena Allah ka hana a yi addu’a gare shi.
5 Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce; kana magana kamar mai wayo.
6 Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba; maganar bakinka za tă juya a kanka.
7 “Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa? Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?
8 Kana sauraron shawarar Allah? Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?
9 Me ka sani da ba mu sani ba? Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?
10 Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu mutanen da sun girme babanka.
11 Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?
12 Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske,
13 har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?
14 “Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki, ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?
15 In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba, in har sammai ba su da tsarki a idonsa,
16 mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa, wanda yake shan mugunta kamar ruwa!
17 “Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani; bari in gaya maka abin da na gani,
18 abin da masu hikima suka ce, ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba
19 (waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar).
20 Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala, wahala kaɗai zai yi ta sha.
21 Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa’yan fashi za su kai masa hari.
22 Yana jin tsoron duhu domin za a kashe shi da takobi.
23 Yana ta yawo, abinci don ungulaye; ya san ranar duhu tana kusa.
24 Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi,
25 domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,
26 ya tasar masa da faɗa da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.
27 “Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu kuma yana da tsoka ko’ina,
28 zai yi gādon garuruwan da suka lalace, da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki, gidajen da sun zama tarkace.
29 Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba, abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.
30 Ba zai tsere wa duhu ba; wuta za tă ƙona rassansa, kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.
31 Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.
32 Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka, kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.
33 Zai zama kamar itacen inabi wanda’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna, kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.
34 Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da’ya’ya, wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.
35 Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta; cikinsu yana cike da ruɗami.”