< Ayuba 14 >
1 “Mutum haihuwar mace kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.
2 Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa; kamar inuwa, ba ya daɗewa.
3 Za ka zura ido a kan irin wannan ne? Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?
4 Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki? Babu!
5 An lissafta kwanakin mutum; ka riga ka ɗibar masa watanni, ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.
6 Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi, ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa.
7 “Aƙalla itace yana da bege. In an sare shi, zai sāke tsira, zai tohu da kyau.
8 Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasa kuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa.
9 Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu yă yi tsiro kamar shuka.
10 Amma mutum yana mutuwa a bizne shi; daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan.
11 Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafi sai wurin yă bushe,
12 haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba; har sai duniya ta shuɗe mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.
13 “Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni! (Sheol )
14 In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa? In haka ne zan daure kwanakin da nake shan wahala har su wuce.
15 Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.
16 Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina amma ba za ka kula da zunubaina ba.
17 Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina.
18 “Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwa su farfashe su kuma gusa daga wurarensu,
19 yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa, haka kake barin mutum ba bege.
20 Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace, ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi.
21 Ko an martaba’ya’yansa maza, ba zai sani ba; Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba.
22 Zafin jikinsa kaɗai yake ji yana kuka wa kansa ne kaɗai.”