< Ayuba 13 >
1 “Idanuna sun ga waɗannan duka, kunnuwana sun ji sun kuma gane.
2 Abin da kuka sani, ni ma na sani; ba ku fi ni ba.
3 Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye.
4 Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!
5 In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.
6 Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina.
7 Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?
8 Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa?
9 In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?
10 Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye.
11 Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba?
12 Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne.
13 “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.
14 Don me na sa kaina cikin hatsari na yi kasada da raina?
15 Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa
16 lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!
17 Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa; bari kunnuwanku su ji abin da zan ce.
18 Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi.
19 Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.
20 “Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;
21 Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.
22 Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.
23 Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina.
24 Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?
25 Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?
26 Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.
27 Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.
28 “Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye.