< Ayuba 11 >

1 Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
ויען צפר הנעמתי ויאמר
2 “Duk surutun nan ba za a amsa maka ba? Ko mai surutun nan marar laifi ne?
הרב דברים לא יענה ואם-איש שפתים יצדק
3 Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?
בדיך מתים יחרישו ותלעג ואין מכלם
4 Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’
ותאמר זך לקחי ובר הייתי בעיניך
5 Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba
ואולם--מי יתן אלוה דבר ויפתח שפתיו עמך
6 yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.
ויגד-לך תעלמות חכמה-- כי-כפלים לתושיה ודע-- כי-ישה לך אלוה מעונך
7 “Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?
החקר אלוה תמצא אם עד-תכלית שדי תמצא
8 Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani? (Sheol h7585)
גבהי שמים מה-תפעל עמקה משאול מה-תדע (Sheol h7585)
9 Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku.
ארכה מארץ מדה ורחבה מני-ים
10 “In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?
אם-יחלף ויסגיר ויקהיל ומי ישיבנו
11 Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?
כי-הוא ידע מתי-שוא וירא-און ולא יתבונן
12 Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.
ואיש נבוב ילבב ועיר פרא אדם יולד
13 “Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,
אם-אתה הכינות לבך ופרשת אליו כפיך
14 in ka kawar da zunubin da yake hannunka, ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba
אם-און בידך הרחיקהו ואל-תשכן באהליך עולה
15 shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba; za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.
כי-אז תשא פניך ממום והיית מצק ולא תירא
16 Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.
כי-אתה עמל תשכח כמים עברו תזכר
17 Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya.
ומצהרים יקום חלד תעפה כבקר תהיה
18 Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
ובטחת כי-יש תקוה וחפרת לבטח תשכב
19 Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
ורבצת ואין מחריד וחלו פניך רבים
20 Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba, kuma ba za su iya tserewa ba; begensu zai zama na mutuwa.”
ועיני רשעים תכלינה ומנוס אבד מנהם ותקותם מפח-נפש

< Ayuba 11 >