< Ayuba 10 >

1 “Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi.
נקטה נפשי בחיי אעזבה עלי שיחי אדברה במר נפשי
2 Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.
אמר אל-אלוה אל-תרשיעני הודיעני על מה-תריבני
3 Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?
הטוב לך כי תעשק--כי-תמאס יגיע כפיך ועל-עצת רשעים הופעת
4 Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?
העיני בשר לך אם-כראות אנוש תראה
5 Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne
הכימי אנוש ימיך אם-שנותיך כימי גבר
6 da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?
כי-תבקש לעוני ולחטאתי תדרוש
7 Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.
על-דעתך כי-לא ארשע ואין מידך מציל
8 “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?
ידיך עצבוני ויעשוני יחד סביב ותבלעני
9 Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?
זכר-נא כי-כחמר עשיתני ואל-עפר תשיבני
10 Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.
הלא כחלב תתיכני וכגבנה תקפיאני
11 Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?
עור ובשר תלבישני ובעצמות וגידים תשככני
12 Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.
חיים וחסד עשית עמדי ופקדתך שמרה רוחי
13 “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.
ואלה צפנת בלבבך ידעתי כי-זאת עמך
14 In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.
אם-חטאתי ושמרתני ומעוני לא תנקני
15 Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.
אם רשעתי אללי לי-- וצדקתי לא-אשא ראשי שבע קלון וראה עניי
16 In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.
ויגאה כשחל תצודני ותשב תתפלא-בי
17 Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina kana ƙara haushinka a kaina; kana ƙara kawo mini hari.
תחדש עדיך נגדי ותרב כעשך עמדי חליפות וצבא עמי
18 “Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata? Da ma na mutu kafin a haife ni.
ולמה מרחם הצאתני אגוע ועין לא-תראני
19 Da ma ba a halicce ni ba, da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!
כאשר לא-הייתי אהיה מבטן לקבר אובל
20 ’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne? Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci
הלא-מעט ימי יחדל (וחדל) ישית (ושית) ממני ואבליגה מעט
21 kafin in koma inda na fito, ƙasa mai duhu da inuwa sosai,
בטרם אלך ולא אשוב-- אל-ארץ חשך וצלמות
22 zuwa ƙasa mai duhun gaske, da inuwa da hargitsi, inda haske yake kamar duhu.”
ארץ עפתה כמו אפל--צלמות ולא סדרים ותפע כמו-אפל

< Ayuba 10 >