< Irmiya 7 >
1 Maganar da ta zo wa Irmiya ke nan daga Ubangiji.
上主有話給耶肋米亞說:
2 “Ka tsaya a ƙofar gidan Ubangiji, a can kuwa ka yi shelar wannan saƙo. “‘Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi don yin sujada ga Ubangiji.
「你站在上主殿字的門口,宣佈這話說:你們凡由這些門進來,朝拜上主的猶大人,請聽上主的話。
3 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri.
萬軍的上主,以色列的這樣說:改善你們的生活和行為,我就讓你們住在這地方;
4 Kada ku dogara ga maganganun nan na ruɗarwa cewa, “Wannan shi ne haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji!”
不要信賴虛偽的話說:「這是上主的聖殿,上主的聖殿,上主的聖殿!
5 In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku,
只有他們徹底改善你的生活和行為,在人與人之間行事公道,
6 in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba,
不虐待旅客、孤兒、寡婦,不在這地方傾流無辜者的血,不自招禍患去跟隨外邦的神祗,
7 to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin.
我才讓你們住在這地方,即我自開始便永遠賜給你們祖先的土地。
8 Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.
可惜! 你們竟信賴虛偽無益的話。
9 “‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba,
怎麼﹖你們竟偷盜,兇殺,通姦,發虛誓,向巴耳獻香,跟隨素不相識的外方神祗,
10 sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?
然後來到這歸我名下的殿裏,立在我面前說:「我們有了保障! 」好再去行這一切可惡的事﹖
11 Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji.
難道這座歸我名下的殿宇,在你們眼中竟成了賊窩了嗎﹖哎! 我看實在是這樣──上主的斷語。
12 “‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila.
那麼,請你們到我昔日在史羅立我名的地方去,察看我因我人名以色列的邪惡對她行了的事
13 Yayinda kuke yin dukan waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji, na yi muku magana sau da sau, amma ba ku ji ba; na kira ku, amma ba ku amsa ba.
現在因為你們做了這一切事──上主的斷語──我再三懇切勸你們,你們又不聽;我呼喚你們,你們也不答應;
14 Saboda haka, abin da na yi wa Shilo shi ne yanzu zan yi wa gidan da ake kira da Sunana, haikalin da kuka dogara a kai, wurin da na ba ku da kuma kakanninku.
為此,我要對付你們依恃的這座歸於我名下的殿宇,並對付我給你們及你們祖先的地域,向對付史羅一樣;
15 Zan kore ku daga gabana, kamar yadda na yi ga dukan’yan’uwanku, mutanen Efraim.’
我必將你們由我面前拋棄,如同拋棄了你們所的有,厄弗辣因全體後裔一樣。
16 “Saboda haka kada ka yi addu’a don wannan mutane ko ka yi wani kuka ko roƙo dominsu, gama ba zan ji ka ba.
至於你,你你不必為這人民祈禱,不必為他們呼籲哀求,也不必向我懇求,因為我不會俯聽你。
17 Ba ka gani abin da suke yi a biranen Yahuda da kuma a titunan Urushalima?
他們在猶大各城和耶路撒冷街上做的是什麼事,難道你沒有看見﹖
18 Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi.
兒子拾柴,父親燒火,母女揉麵給天后做餅,向外方神祗行奠祭,來觸怒我。
19 Amma ni ne suke tsokana? In ji Ubangiji Ashe, ba kansu ne suke cuta, suna kunyata kansu ba?
他們果真觸怒我嗎﹖──上主的斷語──豈不是觸犯自己,使自己滿面慚愧﹖
20 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba.
為此我上主這樣說:看,我的憤怒和怒火,必要傾注在這地方的人和走獸身上,田間的樹木和土地的出產上,燃燒不熄。
21 “‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa ci gaba, ku ƙara hadayun ƙonawarku da sauran sadakoki ku kuma yi ta cin naman!
萬軍的上主,以色列的天主這樣說:「你們獻祭後,儘管飽悢祭肉;
22 Gama sa’ad da na fitar da kakanninku daga Masar na kuma yi musu magana, ban ba su dokoki kawai game da hadayun ƙonawa da sadakoki ba,
可是,關於全燔祭和獻祭的事情,我在領你們祖先出離埃及那一天,並沒有對他們談及或吩咐什麼,
23 amma na ba su wannan umarni cewa ku yi mini biyayya, zan kuwa zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin da na umarce ku, don ku zauna lafiya.
只吩咐了他們這事說:你們應聽從我的聲音,那麼我必作你們的天主,你們也必作我的人民;你們應走我吩咐你們的一切道路,好使你們獲得幸福。
24 Amma ba su saurara ba, ba su kuwa kula ba; a maimako, suka bi shawarar kansu da ta taurare muguwar zukatansu. Su ja da baya a maimakon yin gaba.
他們不但不側耳細聽,反倒依照自己的計劃,隨自己邪惡的心生活,頑固不化;不以面向我,卻以背向我。
25 Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa.
從你們祖先出離埃及那一天起,直到今日,我給你們派遺了我所有的僕人先知,而且每天清早給你們派遺,
26 Amma ba su saurare ni ba, ba su kula ba. Sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.’
但他們不但不側耳聽從我,反而更硬起自己的頸項,比自己的祖先還要乖戾。
27 “Sa’ad da ka faɗa musu wannan duka, ba za su saurare ka ba; sa’ad da ka kira su, ba za su amsa ba.
縱使你將這一切話告訴他們,他們也不會聽從你;任憑你怎樣呼喚,他們也不會答應你。
28 Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Wannan ce al’ummar da ba tă yi biyayya ga Ubangiji Allahnta ba, ba kuwa ta karɓi gyara ba. Gaskiya ta ƙare; ta ɓace gaba ɗaya daga leɓunansu.
為此你對他們說:這個民族,不聽上主自己天主的聲音,不肯接受訓;忠實已喪失,已絕於他們口中。
29 “‘Ku aske gashin kanku ku zubar; ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi’yan zamanin nan ya kuma rabu da su saboda fushin da suka ba shi.
你該剪去你的一綹頭髮,把它拋掉,在高丘上唱哀歌,因為上主擯斥,且拋棄了衪憎恨的時代。
30 “‘Mutanen Yahuda sun yi mugunta a gabana, in ji Ubangiji. Sun kafa gumakansu masu banƙyama a gidan da ake kira da Sunana suka ƙazantar da shi.
的確,猶大子民作了我視為惡的──上主的斷語──將他們可惡之物,安置在歸我名下的殿宇裏,使殿宇受玷污;
31 Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba.
又本希農山谷的托斐特建築了丘壇,為火焚自己的子女;這是我從沒有吩咐,也從沒有想到的事。
32 Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri.
為此,看,時日將到──上主的斷語──人王再稱這地方為「托斐特」,或「本希農谷」,卻要稱它為「屠殺谷」;由於墳地不夠,連斐特也將充作墳場。
33 Sa’an nan gawawwakin wannan mutane za su zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namun jeji, ba za a kuwa sami wani da zai kore su ba.
這人民的屍體將成為天空飛鳥和地上走獸的食物,而沒有人來驅逐。
34 Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai.
我必猶大城內和耶路撒冷街上,再也聽到歡愉和喜樂的音,新郎和新娘的音,因為這地要變為荒野。