< Irmiya 6 >

1 “Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa.
העזו בני בנימן מקרב ירושלם ובתקוע תקעו שופר ועל בית הכרם שאו משאת כי רעה נשקפה מצפון ושבר גדול
2 Zan hallaka Diyar Sihiyona, kyakkyawa da kuma mai laulayi.
הנוה והמענגה דמיתי בת ציון
3 Makiyaya da garkunansu za su taso mata; za su kafa tentunansu kewaye da ita, kowanne yana lura da sashensa.”
אליה יבאו רעים ועדריהם תקעו עליה אהלים סביב רעו איש את ידו
4 “Mu shirya don yaƙi da ita! Ku tashi, bari mu fāɗa mata da tsakar rana! Amma, kaito, rana tana fāɗuwa, inuwar yamma kuwa sai ƙaran tsawo take.
קדשו עליה מלחמה קומו ונעלה בצהרים אוי לנו כי פנה היום כי ינטו צללי ערב
5 Saboda haka ku tashi, bari mu fāɗa mata da dare mu rurrushe kagaranta!”
קומו ונעלה בלילה ונשחיתה ארמנותיה
6 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku sassare itatuwan ku tula ƙasa kewaye da Urushalima. Dole a hukunta wannan birni; saboda ya cika da zalunci.
כי כה אמר יהוה צבאות כרתו עצה ושפכו על ירושלם סללה היא העיר הפקד כלה עשק בקרבה
7 Kamar yadda rijiya takan ba da ruwarta, haka birnin yake da muguntarsa. Ana jin labarin rikici da hallaka a cikinsa; ciwonsa da mikinsa kullum suna a gabana.
כהקיר בור (ביר) מימיה כן הקרה רעתה חמס ושד ישמע בה על פני תמיד--חלי ומכה
8 Ki ji gargaɗi, ya Urushalima, ko kuwa in juya daga gare ki in mai da ƙasarki kufai don kada wani ya zauna a cikinta.”
הוסרי ירושלם--פן תקע נפשי ממך פן אשימך שממה ארץ לוא נושבה
9 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Bari su yi kalan raguwar Isra’ila a yi kalan sarai yadda ake yi wa inabi; ka sāke miƙa hannunka a kan rassan, kamar mai tattara inabi.”
כה אמר יהוה צבאות עולל יעוללו כגפן שארית ישראל השב ידך כבוצר על סלסלות
10 Ga wa zan yi magana in kuma gargaɗar? Wa zai saurare ni? Kunnuwansu sun toshe don kada su ji. Maganar Ubangiji ta zama abin zargi a gare su; ba sa jin daɗinta.
על מי אדברה ואעידה וישמעו--הנה ערלה אזנם ולא יוכלו להקשיב הנה דבר יהוה היה להם לחרפה--לא יחפצו בו
11 Amma ina cike da fushin Ubangiji, kuma ba na iya kannewa. “Ka kwararo shi a kan yara a titi da kuma a kan samarin da suka tattaru; za a kama miji da mata a cikinsa, tsofaffi da suka tsufa tukub.
ואת חמת יהוה מלאתי נלאיתי הכיל--שפך על עולל בחוץ ועל סוד בחורים יחדו כי גם איש עם אשה ילכדו זקן עם מלא ימים
12 Za a ba da gidajensu ga waɗansu, tare da gonakinsu da matansu, sa’ad da na miƙa hannuna gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,” in ji Ubangiji.
ונסבו בתיהם לאחרים שדות ונשים יחדו כי אטה את ידי על ישבי הארץ נאם יהוה
13 “Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya.
כי מקטנם ועד גדולם כלו בוצע בצע ומנביא ועד כהן--כלו עשה שקר
14 Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya.
וירפאו את שבר עמי על נקלה--לאמר שלום שלום ואין שלום
15 Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji.
הבישו כי תועבה עשו גם בוש לא יבושו גם הכלים לא ידעו--לכן יפלו בנפלים בעת פקדתים יכשלו אמר יהוה
16 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba; ku nemi hanyoyin dā, ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta, za ku kuwa sami hutu wa rayukanku. Amma kun ce, ‘Ba za mu bi ta ba.’
כה אמר יהוה עמדו על דרכים וראו ושאלו לנתבות עולם אי זה דרך הטוב ולכו בה ומצאו מרגוע לנפשכם ויאמרו לא נלך
17 Na naɗa muku masu tsaro a kanku na kuma ce, ‘Ku saurari karan ƙaho!’ Amma kuka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’
והקמתי עליכם צפים הקשיבו לקול שופר ויאמרו לא נקשיב
18 Saboda haka ku, ya al’ummai; ku lura Ya shaidu, abin da zai faru da su.
לכן שמעו הגוים ודעי עדה את אשר בם
19 Ki ji, ya duniya. Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane, sakayyar ƙulle-ƙullensu, domin ba su saurari maganata ba suka kuma ƙi dokata.
שמעי הארץ--הנה אנכי מביא רעה אל העם הזה פרי מחשבותם כי על דברי לא הקשיבו ותורתי וימאסו בה
20 Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.”
למה זה לי לבונה משבא תבוא וקנה הטוב מארץ מרחק עלותיכם לא לרצון וזבחיכם לא ערבו לי
21 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena. Mahaifi da’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna; maƙwabci da abokansa za su hallaka.”
לכן כה אמר יהוה הנני נתן אל העם הזה מכשלים וכשלו בם אבות ובנים יחדו שכן ורעו--יאבדו (ואבדו)
22 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Duba, sojoji suna zuwa daga ƙasar arewa; babbar al’umma ce ta yunƙuro daga iyakokin duniya.
כה אמר יהוה הנה עם בא מארץ צפון וגוי גדול יעור מירכתי ארץ
23 Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne kuma marasa tausayi. Motsinsu kamar ƙugin teku ne yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa a jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Sihiyona.”
קשת וכידון יחזיקו אכזרי הוא ולא ירחמו קולם כים יהמה ועל סוסים ירכבו ערוך כאיש למלחמה עליך בת ציון
24 Mun ji labari a kansu, hannuwanmu kuwa suka yi laƙwas. Azaba ta kama mu, zafi kamar na mace mai naƙuda.
שמענו את שמעו רפו ידינו צרה החזקתנו--חיל כיולדה
25 Kada ku fita zuwa gonaki ko ku yi tafiya a hanyoyi, gama abokin gāba yana da takobi, kuma akwai razana ko’ina.
אל תצאי (תצאו) השדה ובדרך אל תלכי (תלכו) כי חרב לאיב מגור מסביב
26 Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki ku yi birgima a toka; ku yi kuka mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, gama nan da nan mai hallakarwa zai auko mana.
בת עמי חגרי שק והתפלשי באפר--אבל יחיד עשי לך מספד תמרורים כי פתאם יבא השדד עלינו
27 “Na maishe ka mai jarrabawar ƙarfe mutanena ne kuwa ƙarfen, don ka lura ka kuma gwada hanyoyinsu.
בחון נתתיך בעמי מבצר ותדע ובחנת את דרכם
28 Su duka masu taurinkai ne,’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne.
כלם סרי סוררים הלכי רכיל נחשת וברזל כלם משחיתים המה
29 Mazuga yana zuga da ƙarfi don yă ƙone dalma da wuta, amma tacewa yana tafiya a banza; ba a fitar da mugaye.
נחר מפח מאשתם (מאש תם) עפרת--לשוא צרף צרוף ורעים לא נתקו
30 Ana ce da su azurfar da aka ƙi, gama Ubangiji ya ƙi su.”
כסף נמאס קראו להם כי מאס יהוה בהם

< Irmiya 6 >