< Irmiya 52 >

1 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal,’yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna.
בן עשרים ואחת שנה צדקיהו במלכו ואחת עשרה שנה מלך בירושלם ושם אמו חמיטל (חמוטל) בת ירמיהו מלבנה
2 Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi.
ויעש הרע בעיני יהוה ככל אשר עשה יהויקם
3 Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon.
כי על אף יהוה היתה בירושלם ויהודה עד השליכו אותם מעל פניו וימרד צדקיהו במלך בבל
4 A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita.
ויהי בשנה התשעית למלכו בחדש העשירי בעשור לחדש בא נבוכדראצר מלך בבל הוא וכל חילו על ירושלם ויחנו עליה ויבנו עליה דיק סביב
5 An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.
ותבא העיר במצור עד עשתי עשרה שנה למלך צדקיהו
6 A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.
בחדש הרביעי בתשעה לחדש ויחזק הרעב בעיר ולא היה לחם לעם הארץ
7 Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.
ותבקע העיר וכל אנשי המלחמה יברחו ויצאו מהעיר לילה דרך שער בין החמתים אשר על גן המלך וכשדים על העיר סביב וילכו דרך הערבה
8 Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi.
וירדפו חיל כשדים אחרי המלך וישיגו את צדקיהו בערבת ירחו וכל חילו--נפצו מעליו
9 Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a.
ויתפשו את המלך ויעלו אתו אל מלך בבל רבלתה בארץ חמת וידבר אתו משפטים
10 Sarkin Babilon ya kashe’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla.
וישחט מלך בבל את בני צדקיהו לעיניו וגם את כל שרי יהודה שחט ברבלתה
11 Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.
ואת עיני צדקיהו עור ויאסרהו בנחשתים ויבאהו מלך בבל בבלה ויתנהו בבית (בית) הפקדת עד יום מותו
12 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.
ובחדש החמישי בעשור לחדש היא שנת תשע עשרה שנה למלך נבוכדראצר מלך בבל--בא נבוזראדן רב טבחים עמד לפני מלך בבל בירושלם
13 Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima.
וישרף את בית יהוה ואת בית המלך ואת כל בתי ירושלם ואת כל בית הגדול שרף באש
14 Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima.
ואת כל חמות ירושלם סביב נתצו כל חיל כשדים אשר את רב טבחים
15 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.
ומדלות העם ואת יתר העם הנשארים בעיר ואת הנפלים אשר נפלו אל מלך בבל ואת יתר האמון--הגלה נבוזראדן רב טבחים
16 Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.
ומדלות הארץ--השאיר נבוזראדן רב טבחים לכרמים וליגבים
17 Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon.
ואת עמודי הנחשת אשר לבית יהוה ואת המכנות ואת ים הנחשת אשר בבית יהוה--שברו כשדים וישאו את כל נחשתם בבלה
18 Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali.
ואת הסרות ואת היעים ואת המזמרות ואת המזרקת ואת הכפות ואת כל כלי הנחשת אשר ישרתו בהם--לקחו
19 Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.
ואת הספים ואת המחתות ואת המזרקות ואת הסירות ואת המנרות ואת הכפות ואת המנקיות אשר זהב זהב ואשר כסף כסף--לקח רב טבחים
20 Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.
העמודים שנים הים אחד והבקר שנים עשר נחשת אשר תחת המכנות אשר עשה המלך שלמה לבית יהוה--לא היה משקל לנחשתם כל הכלים האלה
21 Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki.
והעמודים שמנה עשרה אמה קומה (קומת) העמד האחד וחוט שתים עשרה אמה יסבנו ועביו ארבע אצבעות נבוב
22 A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman.
וכתרת עליו נחשת וקומת הכתרת האחת חמש אמות ושבכה ורמונים על הכותרת סביב הכל נחשת וכאלה לעמוד השני ורמונים
23 Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.
ויהיו הרמנים--תשעים וששה רוחה כל הרמונים מאה על השבכה סביב
24 Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su.
ויקח רב טבחים את שריה כהן הראש ואת צפניה כהן המשנה--ואת שלשת שמרי הסף
25 Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su.
ומן העיר לקח סריס אחד אשר היה פקיד על אנשי המלחמה ושבעה אנשים מראי פני המלך אשר נמצאו בעיר ואת ספר שר הצבא המצבא את עם הארץ וששים איש מעם הארץ הנמצאים בתוך העיר
26 Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla,
ויקח אותם נבוזראדן רב טבחים וילך אותם אל מלך בבל רבלתה
27 Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta.
ויכה אותם מלך בבל וימתם ברבלה בארץ חמת ויגל יהודה מעל אדמתו
28 Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa 3,023;
זה העם אשר הגלה נבוכדראצר בשנת שבע--יהודים שלשת אלפים ועשרים ושלשה
29 a shekara ta goma sha takwas ta sarautar Nebukadnezzar, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima 832;
בשנת שמונה עשרה לנבוכדראצר מירושלם--נפש שמנה מאות שלשים ושנים
30 a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745. Jimillarsu duka 4,600 ne.
בשנת שלש ועשרים לנבוכדראצר הגלה נבוזראדן רב טבחים יהודים נפש שבע מאות ארבעים וחמשה כל נפש ארבעת אלפים ושש מאות
31 A shekarar da Ewil-Merodak ya zama Sarkin Babilon, sai ya nuna wa Yehohiyacin Sarkin Yahuda alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yehohiyacin bauta.
ויהי בשלשים ושבע שנה לגלות יהויכן מלך יהודה בשנים עשר חדש בעשרים וחמשה לחדש נשא אויל מרדך מלך בבל בשנת מלכתו את ראש יהויכין מלך יהודה ויצא אתו מבית הכליא (הכלוא)
32 Ewil-Merodak ya nuna wa Yehohiyacin alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babilon tare da shi.
וידבר אתו טבות ויתן את כסאו ממעל לכסא מלכים (המלכים) אשר אתו בבבל
33 Yehohiyacin ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa.
ושנה את בגדי כלאו ואכל לחם לפניו תמיד כל ימי חיו
34 Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarkin Babilon, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.
וארחתו ארחת תמיד נתנה לו מאת מלך בבל דבר יום ביומו--עד יום מותו כל ימי חייו

< Irmiya 52 >