< Irmiya 51 >

1 Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan zuga ruhun mai hallakarwa a kan Babilon da mutanen Leb Kamai.
כה אמר יהוה הנני מעיר על בבל ואל ישבי לב קמי--רוח משחית
2 Zan aika da baƙi zuwa Babilon su casa ta su kuma yi kaca-kaca da ƙasarta; za su yi hamayya da ita a kowane gefe a ranar masifarta.
ושלחתי לבבל זרים וזרוה ויבקקו את ארצה כי היו עליה מסביב ביום רעה
3 Kada ku bar maharbi yă ja bakansa, kada kuma ku bari yă sa kayan yaƙinsa. Kada ku rage samarinta, ku hallaka sojojinta ƙaf.
אל ידרך ידרך הדרך קשתו ואל יתעל בסרינו ואל תחמלו אל בחריה--החרימו כל צבאה
4 Za su fāɗi matattu a ƙasar Babilon, da munanan raunuka a titunanta.
ונפלו חללים בארץ כשדים ומדקרים בחוצותיה
5 Gama Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila da Yahuda bai yashe su ba, ko da yake ƙasarsu cike da take da laifi a gaban Mai Tsarki na Isra’ila.
כי לא אלמן ישראל ויהודה מאלהיו--מיהוה צבאות כי ארצם מלאה אשם מקדוש ישראל
6 “Ku gudu daga cikin Babilon! Bari kowa yă ceci ransa! Kada a hallaka saboda zunubanta. Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji, zai sāka mata bisa ga alhakinta.
נסו מתוך בבל ומלטו איש נפשו--אל תדמו בעונה כי עת נקמה היא ליהוה--גמול הוא משלם לה
7 Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashe sun sha ruwan inabinta, saboda haka yanzu sun haukace.
כוס זהב בבל ביד יהוה--משכרת כל הארץ מיינה שתו גוים על כן יתהללו גוים
8 Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe. Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani saboda azabarta; wataƙila za a iya warkar da ita.
פתאם נפלה בבל ותשבר הילילו עליה קחו צרי למכאובה--אולי תרפא
9 “‘Da mun warkar da Babilon, amma ba za tă warke ba; mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu, gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo kamar gizagizai.’
רפאנו את בבל ולא נרפתה--עזבוה ונלך איש לארצו כי נגע אל השמים משפטה ונשא עד שחקים
10 “‘Ubangiji ya baratar da mu; zo mu tafi mu yi shelarsa a Sihiyona mu faɗa abin da Ubangiji Allahnmu ya yi.’
הוציא יהוה את צדקתינו באו ונספרה בציון את מעשה יהוה אלהינו
11 “Ku wasa kibiyoyi, ku ɗauko garkuwoyi! Ubangiji ya zuga sarakunan Medes, domin niyyarsa ce yă hallaka Babilon. Ubangiji zai yi ramuwa, zai yi ramuwa saboda haikalinsa.
הברו החצים מלאו השלטים--העיר יהוה את רוח מלכי מדי כי על בבל מזמתו להשחיתה כי נקמת יהוה היא נקמת היכלו
12 Ku tā da tuta gāba da katangan Babilon! Ku ƙara matsara, ku kafa masu tsaro, ku shirya kwanto! Ga shi, Ubangiji zai aikata abin da ya faɗa umarninsa a kan mutanen Babilon.
אל חומת בבל שאו נס החזיקו המשמר--הקימו שמרים הכינו הארבים כי גם זמם יהוה--גם עשה את אשר דבר אל ישבי בבל
13 Ke da kike zama kusa da ruwaye da kike kuma wadatar dukiya, ƙarshenki ya zo, lokaci ya yi da za a kau da ke.
שכנתי (שכנת) על מים רבים רבת אוצרת בא קצך אמת בצעך
14 Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra, za su kuwa yi sowa don nasara a kanka.
נשבע יהוה צבאות בנפשו כי אם מלאתיך אדם כילק וענו עליך הידד
15 “Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
עשה ארץ בכחו מכין תבל בחכמתו ובתבונתו נטה שמים
16 Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa.
לקול תתו המון מים בשמים ויעל נשאים מקצה ארץ ברקים למטר עשה ויוצא רוח מאצרתיו
17 “Kowane mutum marar azanci ne kuma ba shi da sani; kowane maƙerin zinariya yakan sha kunya daga wurin gumakansa. Siffofinsa na ƙarya ne; babu numfashi a cikinsu.
נבער כל אדם מדעת הביש כל צרף מפסל כי שקר נסכו ולא רוח בם
18 Su marasa amfani ne, abubuwan ba’a ne kawai; sa’ad da lokacin hukuncinsu ya kai, za su hallaka.
הבל המה מעשה תעתעים בעת פקדתם יאבדו
19 Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne, gama shi ne Mahalicci dukan abu, har da kabilar abin gādonsa, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
לא כאלה חלק יעקוב כי יוצר הכל הוא--ושבט נחלתו יהוה צבאות שמו
20 “Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki,
מפץ אתה לי כלי מלחמה ונפצתי בך גוים והשחתי בך ממלכות
21 da kai ne na ragargaza doki da mahayi, da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi,
ונפצתי בך סוס ורכבו ונפצתי בך רכב ורכבו
22 da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa,
ונפצתי בך איש ואשה ונפצתי בך זקן ונער ונפצתי בך בחור ובתולה
23 da kai ne na ragargaza makiyayi da garke, da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma, da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni.
ונפצתי בך רעה ועדרו ונפצתי בך אכר וצמדו ונפצתי בך פחות וסגנים
24 “Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji.
ושלמתי לבבל ולכל יושבי כשדים את כל רעתם אשר עשו בציון--לעיניכם נאם יהוה
25 “Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse.
הנני אליך הר המשחית נאם יהוה המשחית את כל הארץ ונטיתי את ידי עליך וגלגלתיך מן הסלעים ונתתיך להר שרפה
26 Ba za a ɗauki dutsen yin kusurwa daga gare ki ba ko na kafa harsashen gini, gama za ki zama marar amfani har abada,” in ji Ubangiji.
ולא יקחו ממך אבן לפנה ואבן למוסדות כי שממות עולם תהיה נאם יהוה
27 “Ku tā da tuta a ƙasa! Ku busa ƙahoni a cikin ƙasashe! Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, ku kira waɗannan mulkokin gāba da ita. Ararat, Minni, da Ashkenaz. A naɗa shugaba gāba da ita; ku shirya dawakai kamar fāra.
שאו נס בארץ תקעו שופר בגוים קדשו עליה גוים--השמיעו עליה ממלכות אררט מני ואשכנז פקדו עליה טפסר העלו סוס כילק סמר
28 Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, sarakunan Medes, gwamnoninsu da dukan masu shugabancinsu da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.
קדשו עליה גוים את מלכי מדי את פחותיה ואת כל סגניה ואת כל ארץ ממשלתו
29 Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata, nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai don kada kowa yă zauna a can.
ותרעש הארץ ותחל כי קמה על בבל מחשבות יהוה לשום את ארץ בבל לשמה מאין יושב
30 Sojojin Babilon sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata. An sa wa wuraren zamanta wuta, an karya ƙyamaren ƙofofin garinta.
חדלו גבורי בבל להלחם ישבו במצדות--נשתה גבורתם היו לנשים הציתו משכנתיה נשברו בריחיה
31 Maguji yana biye da maguji a guje, jakada yana biye da jakada, don su faɗa wa sarkin Babilon, cewa an ci birninsa a kowane gefe.
רץ לקראת רץ ירוץ ומגיד לקראת מגיד--להגיד למלך בבל כי נלכדה עירו מקצה
32 An ƙwace mashigai aka ƙone fadamu da wuta, sojoji kuma suka giggice.”
והמעברות נתפשו ואת האגמים שרפו באש ואנשי המלחמה נבהלו
33 Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce, “’Yar Babilon kamar daɓen masussuka a lokacin da ake sussuka, ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
כי כה אמר יהוה צבאות אלהי ישראל בת בבל כגרן עת הדריכה עוד מעט ובאה עת הקציר לה
34 “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu, ya sa muka rikice, ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa. Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu, sa’an nan kuma ya yi amanmu.
אכלנו (אכלני) הממנו (הממני) נבוכדראצר מלך בבל הציגנו (הציגני) כלי ריק בלענו (בלעני) כתנין מלא כרשו מעדני הדיחנו (הדיחני)
35 Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,” in ji mazaunan Sihiyona. “Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,” in ji Urushalima.
חמסי ושארי על בבל תאמר ישבת ציון ודמי אל ישבי כשדים תאמר ירושלם
36 Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “Duba, zan tsaya muku, zan ɗaukar muku fansa, zan sa tekunta kafe in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe.
לכן כה אמר יהוה הנני רב את ריבך ונקמתי את נקמתך והחרבתי את ימה והבשתי את מקורה
37 Babilon za tă zama tarin juji, wurin zaman diloli, abin ƙyama da abar ba’a, inda ba kowa.
והיתה בבל לגלים מעון תנים שמה ושרקה מאין יושב
38 Mutanenta duk suna ruri kamar zakoki, suna gurnani kamar’ya’yan zaki.
יחדו ככפרים ישאגו נערו כגורי אריות
39 Amma sa’ad da aka farkar da su, zan yi musu biki in sa su sha su bugu, domin yi sowa da dariya, sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,” in ji Ubangiji.
בחמם אשית את משתיהם והשכרתים למען יעלזו וישנו שנת עולם ולא יקיצו--נאם יהוה
40 “Zan sauko da su kamar tumaki zuwa mayanka, kamar raguna da bunsurai.
אורידם ככרים לטבוח--כאילים עם עתודים
41 “Yadda za a ci Sheshak, taƙamar duniya duka za tă daina! Babilon za tă zama abar ƙyama a cikin al’ummai!
איך נלכדה ששך ותתפש תהלת כל הארץ איך היתה לשמה בבל בגוים
42 Teku zai malalo a kan Babilon, raƙumansa masu hauka za su rufe ta.
עלה על בבל הים בהמון גליו נכסתה
43 Garuruwanta sun zama abin kufai, za tă zama hamada inda ba ruwa, ƙasar da ba mazauna, ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.
היו עריה לשמה ארץ ציה וערבה ארץ לא ישב בהן כל איש ולא יעבר בהן בן אדם
44 Zan hukunta Bel a Babilon, in sa ya yi aman abin da ya haɗiye. Ƙasashe ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Katangan Babilon kuwa za tă rushe!
ופקדתי על בל בבבל והצאתי את בלעו מפיו ולא ינהרו אליו עוד גוים גם חומת בבל נפלה
45 “Ku fito daga cikinta, jama’ata! Ku tsere da ranku! Ku tsere daga zafin fushin Ubangiji.
צאו מתוכה עמי ומלטו איש את נפשו--מחרון אף יהוה
46 Kada zuciyarku tă yi suwu ko ku ji tsoro sa’ad da aka ji labarin a ƙasar, labari guda a wannan shekara, wani kuma a ta biye, labarin hargitsi a ƙasar mai mulki ya tasar wa mai mulki.
ופן ירך לבבכם ותיראו בשמועה הנשמעת בארץ ובא בשנה השמועה ואחריו בשנה השמועה וחמס בארץ ומשל על משל
47 Gama kwanaki tabbatacce suna zuwa, sa’ad da zan hukunta gumakan Babilon, zan kunyatar da dukan ƙasar kuma matattunta duk za su kwanta a cikinta.
לכן הנה ימים באים ופקדתי על פסילי בבל וכל ארצה תבוש וכל חלליה יפלו בתוכה
48 Sa’an nan sama da ƙasa da dukan abin da yake cikinsu, za su yi sowa ta murna a kan Babilon, gama daga arewa masu hallakarwa su auko mata,” in ji Ubangiji.
ורננו על בבל שמים וארץ וכל אשר בהם כי מצפון יבוא לה השודדים נאם יהוה
49 “Babilon za tă fāɗi saboda kisassun mutanen Isra’ila, kamar dai yadda kisassu dukan duniya suka fāɗi saboda Babilon.
גם בבל לנפל חללי ישראל גם לבבל נפלו חללי כל הארץ
50 Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.”
פלטים מחרב הלכו אל תעמדו זכרו מרחוק את יהוה וירושלם תעלה על לבבכם
51 “Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana kunya ta rufe mu, domin baƙi sun shiga tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.”
בשנו כי שמענו חרפה כסתה כלמה פנינו כי באו זרים על מקדשי בית יהוה
52 “Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta gumakanta, da kuma a dukan ƙasarta waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.
לכן הנה ימים באים נאם יהוה ופקדתי על פסיליה ובכל ארצה יאנק חלל
53 Ko da Babilon za tă kai sararin sama ne, ta gina kagaranta mai ƙarfi, duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta,” in ji Ubangiji.
כי תעלה בבל השמים וכי תבצר מרום עזה מאתי יבאו שדדים לה--נאם יהוה
54 “Ku ji muryar kuka daga Babilon, Da hargowar babbar hallakarwa daga ƙasar Babiloniyawa!
קול זעקה מבבל ושבר גדול מארץ כשדים
55 Gama Ubangiji zai rushe Babilon, zai sa ta ƙame bakinta na alfarma. Sojoji za su yi ta kutsawa kamar raƙuman ruwa; suna tā da muryoyinsu.
כי שדד יהוה את בבל ואבד ממנה קול גדול והמו גליהם כמים רבים נתן שאון קולם
56 Gama mai hallakarwa ya auka wa Babilon, a kama sojojinta, a kuma kakkarya bakkunansu. Gama Ubangiji shi Allah ne mai sakayya; zai yi sakayya sosai.
כי בא עליה על בבל שודד ונלכדו גבוריה חתתה קשתותם כי אל גמלות יהוה שלם ישלם
57 Zan sa mahukuntanta da masu hikimarta, gwamnoninta, shugabanninta da sojojinta su sha su bugu; za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” in ji Sarkin, mai suna Ubangiji Maɗaukaki.
והשכרתי שריה וחכמיה פחותיה וסגניה וגבוריה וישנו שנת עולם ולא יקיצו נאם המלך--יהוה צבאות שמו
58 Ni Ubangiji Maɗaukaki, na ce, “Za a baje katangan nan na Babilon mai kauri za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta; mutane sun wahalar da kansu a banza, al’umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”
כה אמר יהוה צבאות חמות בבל הרחבה ערער תתערער ושעריה הגבהים באש יצתו ויגעו עמים בדי ריק ולאמים בדי אש ויעפו
59 Jawabin da annabi Irmiya ya ba Serahiya, ɗan Neriya, wato, jikan Ma’asehiya, lokacin da ya tafi tare da Zedekiya, Sarkin Yahuda, zuwa Babilon a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Serahiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.
הדבר אשר צוה ירמיהו הנביא את שריה בן נריה בן מחסיה בלכתו את צדקיהו מלך יהודה בבל בשנת הרבעית למלכו ושריה שר מנוחה
60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babilon, wato, dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babilon.
ויכתב ירמיהו את כל הרעה אשר תבוא אל בבל--אל ספר אחד את כל הדברים האלה הכתבים אל בבל
61 Irmiya kuwa ya ce wa Serahiya, “Lokacin da ka kai Babilon, sai ka karanta dukan maganan nan.
ויאמר ירמיהו אל שריה כבאך בבל--וראית וקראת את כל הדברים האלה
62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’
ואמרת יהוה אתה דברת אל המקום הזה להכריתו לבלתי היות בו יושב למאדם ועד בהמה כי שממות עולם תהיה
63 Sa’ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa’an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yuferites.
והיה ככלתך לקרא את הספר הזה תקשר עליו אבן והשלכתו אל תוך פרת
64 Sa’an nan ka ce, ‘Haka Babilon za tă nutse, ba za tă ƙara tashi ba saboda masifar da zan kawo mata. Mutanenta kuwa za su fāɗi.’” Wannan shi ne ƙarshen kalmomin Irmiya.
ואמרת ככה תשקע בבל ולא תקום מפני הרעה אשר אנכי מביא עליה--ויעפו עד הנה דברי ירמיהו

< Irmiya 51 >