< Irmiya 50 >

1 Ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Irmiya annabi game da Babilon da kuma ƙasar Babiloniyawa.
Palabra que Yahvé dirigió a Babilonia, a la tierra de los caldeos, por boca del profeta Jeremías:
2 “Ka yi shela ka kuma furta a cikin al’ummai, ka tā da tuta ka kuma furta; kada ku ɓoye kome, amma ku ce, ‘Za a ci Babilon da yaƙi; za a kunyata Bel, Marduk ya cika da tsoro. Siffofinta za su sha kunya gumakanta za su cika da tsoro.’
“Publicadlo entre los pueblos, pregonadlo; alzad bandera, proclamadlo, no lo encubráis; decid: «Tomada ha sido Babilonia; avergonzado está Bel y abatido Merodac. Sus simulacros están cubiertos de ignominia, sus ídolos tiemblan de terror».
3 Al’umma daga arewa za tă fāɗa mata su mai da ƙasar kango. Ba wanda zai zauna a cikinta; mutane da dabbobi za su gudu.
Pues desde el Septentrión marcha contra ella una nación, que hará de su tierra una soledad sin habitantes; hombres y bestias huyeron, se marcharon.
4 “A kwanakin nan, a wannan lokaci,” in ji Ubangiji, “mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗaya za su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu.
En aquellos días y en aquel tiempo, dice Yahvé, vendrán los hijos de Israel, y con ellos los hijos de Judá; vendrán llorando y buscando a Yahvé, su Dios.
5 Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su kuma juya fuskokinsu wajenta. Za su zo su haɗa kansu ga Ubangiji a madawwamin alkawari da ba za a manta da shi ba.
Preguntarán por el camino de Sión, dirigiendo hacia allá sus rostros, (y diciendo): «Vamos y liguémonos con Yahvé en alianza eterna, que nunca será borrada.»
6 “Mutanena sun zama ɓatattun tumaki; makiyayansu sun bauɗar da su suka sa suna ta yawo a cikin duwatsu. Sun yi ta yawo a bisa dutse da tudu suka manta wurin hutunsu.
Mi pueblo ha venido a ser un rebaño de ovejas perdidas, sus pastores lo han descarriado; por los montes lo hicieron ir vagando; y andando de monte en collado se han olvidado del aprisco.
7 Duk wanda ya same su ya cinye su; abokan gābansu suka ce, ‘Ba mu da laifi, gama sun yi zunubi wa Ubangiji, wurin kiwonsu na gaske, Ubangiji, abin sa zuciyar kakanninsu.’
Cuantos los hallaban, los devoraban; y sus opresores se decían: «No hacemos mal, pues han pecado contra Yahvé, la morada de justicia; contra Yahvé, la esperanza de sus padres.»
8 “Ku gudu daga Babilon; ku bar ƙasar Babiloniyawa, ku zama kamar awakin da suke bi da garke.
Huid de en medio de Babel, y salid del país de los caldeos, sed como los carneros que van delante del rebaño.
9 Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon haɗinkan manyan al’ummai na arewa. Za su ja dāgār gāba da ita, kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi. Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa waɗanda ba sa dawowa hannu wofi.
Pues he aquí que Yo suscitaré y lanzaré contra Babel una multitud de grandes naciones desde el país del Norte, se apostarán contra ella, y de ese lado será tomada; sus flechas son como de hábil guerrero; no vuelven vacías.
10 Saboda haka za a washe Babiloniyawa; dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,” in ji Ubangiji.
Y Caldea será saqueada; todos sus saqueadores se hartarán”, dice Yahvé.
11 “Saboda kuna farin ciki kuna kuma murna, ku da kuka washe gādona, domin kuna tsalle kamar karsana mai sussuka hatsi kuna kuma haniniya kamar ingarmu.
Aunque os alegráis y saltáis de gozo, oh saqueadores de mi herencia; aunque brincáis como novilla en la hierba y relincháis como caballos,
12 Mahaifiyarku za tă sha babbar kunya; ita da ta haife ku za tă sha kunya. Za tă zama mafi ƙanƙanta na al’ummai, jeji, busasshiyar ƙasa, hamada.
quedará muy avergonzada vuestra madre, será cubierta de ignominia la que os dio a luz. He aquí que será la última de las naciones, desierto, tierra árida, estepa.
13 Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta ba amma za tă zama kufai gaba ɗaya. Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsaki saboda dukan mikinta.
A causa de la ira de Yahvé no será habitada, y toda ella se convertirá en soledad. Cuantos pasaren junto a Babilonia, se pasmarán y harán rechifla de todas sus plagas.
14 “Ku ja dāgā kewaye da Babilon, dukanku waɗanda kuke jan baka. Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi, gama ta yi zunubi ga Ubangiji.
Tomad posiciones contra Babilonia a la redonda; los que tendéis el arco, tirad contra ella, no escatiméis las flechas, porque ha pecado contra Yahvé.
15 Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe! Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi, katangarta sun rushe. Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji, ku ɗauki fansa a kanta; yi mata yadda ta yi wa waɗansu.
Alzad contra ella el grito por todos lados; se rinde ya, caen sus baluartes, derribados están sus muros. Es la venganza de Yahvé; tomad venganza de ella; tratadla como ella os ha tratado a vosotros.
16 Ku datse wa Babilon mai shuka, da mai girbi lauje a lokacin girbi. Saboda takobin mai zalunci bari kowa ya koma ga mutanensa, bari kowa ya gudu zuwa ga ƙasarsa.
Exterminad de Babilonia al que siembra, y al que maneja la hoz en el tiempo de la siega. Ante la espada destructora vuélvase cada cual a su pueblo, y huya cada uno a su tierra.
17 “Isra’ila garke ne da ya watse da zakoki suka kora. Na farkon da ya cinye shi sarkin Assuriya ne; na ƙarshen da ya ragargaza ƙasusuwansa Nebukadnezzar sarkin Babilon ne.”
Un rebaño descarriado es Israel, lo dispersaron los leones. Primero lo devoró el rey de Asiria, y el último ha sido este Nabucodonosor, rey de Babel, que le rompió los huesos.
18 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Zan hukunta sarkin Babilon da ƙasarsa yadda na hukunta sarkin Assuriya.
Por tanto, así dice Yahvé de los ejércitos, el Dios de Israel: “He aquí que Yo castigaré al rey de Babilonia y su tierra al modo que castigué al rey de Asiria.
19 Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan; zai ƙosar da marmarinsa a tuddan Efraim da Gileyad.
Traeré a Israel a sus pastizales, y pacerá en el Carmelo y en Basán; sobre las montañas de Efraím y de Galaad se saciará.
20 A kwanakin nan, da kuma a lokacin nan,” in ji Ubangiji, “za a yi bincike don laifin Isra’ila, amma ba za a samu ba, kuma don zunubin Yahuda, amma ba za a sami wani abu ba, gama zan gafarta wa raguwar da na rage.
En aquellos días y en aquel tiempo, dice Yahvé, se buscará la iniquidad de Israel, y no se hallará; y los pecados de Judá, y no se encontrarán, porque seré propicio al resto que haya dejado.
21 “Ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da waɗanda suke zama a Fekod. Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,” in ji Ubangiji. “Ku aikata dukan abin da na umarce ku.
¡Sube contra la tierra de las rebeliones, sube contra ella y sus habitantes (que merecen) castigo! ¡Devasta y extirpa sus restos, dice Yahvé, y haz conforme a cuanto te tengo mandado!”
22 Hargowar yaƙi tana a ƙasar, hargowar babbar hallaka!
¡Estruendo de guerra en la tierra, y ruina tremenda!
23 Dubi yadda aka karya aka kuma ragargaza gudumar dukan duniya! Dubi yadda Babilon ta zama kufai a cikin al’ummai!
¡Cómo ha sido roto y quebrado el martillo de toda la tierra! ¡Cómo ha venido a ser Babilonia un objeto de horror en medio de las naciones!
24 Na sa miki tarko, Babilon, kika kuwa kamu kafin ki sani; aka same ki aka kuma kama ki domin kin tayar wa Ubangiji.
Te he tendido un lazo, y quedaste presa, oh Babilonia, sin darte cuenta. Fuiste sorprendida y tomada, porque hiciste guerra contra Yahvé.
25 Ubangiji ya buɗe taskar makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi a ƙasar Babiloniyawa.
Abrió Yahvé su arsenal y sacó las armas de su indignación; porque el Señor, Yahvé de los ejércitos, quiere ejecutar una obra en el país de los caldeos.
26 Ku zo ku yi gāba da ita daga nesa. Ku buɗe rumbunanta; ku jibga ta kamar tsibin hatsi. Ku hallaka ta sarai kada ku bar mata raguwa.
¡Venid contra ella desde los cabos (del mundo), abrid sus graneros, haced de (sus piedras) montones como gavillas y exterminadla; no le quede ni siquiera un resto!
27 Ku kashe dukan’yan bijimanta bari su gangara zuwa mayanka! Kaitonsu! Gama ranansu ta zo, lokaci ya yi da za a hukunta su.
Matad a todos sus toros, sean conducidos al matadero. ¡Ay de ellos, pues ha llegado su día, el tiempo de su castigo!
28 Ku saurari masu gudun hijira da masu neman mafaka daga Babilon suna furtawa a Sihiyona yadda Ubangiji Allahnmu ya ɗauki fansa, fansa domin haikalinsa.
Se oye la voz de fugitivos que escapan de la tierra de Babel, para anunciar en Sión la venganza de Yahvé, nuestro Dios, la venganza de su Templo.
29 “Ku kira’yan baka a kan Babilon, dukan waɗanda suke jan baka. Ku yi sansani kewaye da ita duka; kada ku bar wani ya tsira. Ku sāka mata don ayyukanta; ku yi mata yadda ta yi. Gama ta tayar wa Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Convocad contra Babilonia a muchos (pueblos), a todos los que entesan el arco; acampad contra ella a la redonda, para que nadie escape; dadle el pago de sus obras; haced con ella conforme a cuanto ella ha hecho, pues se ha alzado contra Yahvé, contra el Santo de Israel.
30 Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna; za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,” in ji Ubangiji.
“Por eso caerán en sus plazas sus jóvenes, y todos sus guerreros perecerán en aquel día, dice Yahvé.
31 “Ga shi, ina gāba da ke, ya ke mai girman kai,” in ji Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, “gama ranarki ta zo, lokacin da za a hukunta ki.
Heme aquí contra ti, oh soberbio, dice el Señor, Yahvé de los ejércitos; pues ha llegado tu día, el tiempo de tu castigo.
32 Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗi kuma ba wanda zai taimake ta tă tashi; zan hura wuta a garuruwanta da za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.”
Tropezará el soberbio y caerá, sin que haya quien le levante; pues pegaré fuego a sus ciudades que devorará todos sus alrededores.”
33 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda. Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan, suna kin barinsu su tafi.
Así dice Yahvé de los ejércitos: “Viven oprimidos los hijos de Israel juntamente con los hijos de Judá, y todos los que los cautivaron los retienen y rehúsan soltarlos.
34 Duk da haka Mai Fansarsu yana da ƙarfi; Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Zai kāre muradunsu gabagadi don yă kawo hutu ga ƙasarsu, amma rashin hutu ga waɗanda suke zaune a Babilon.
Pero su libertador es fuerte, Yahvé de los ejércitos es su nombre; Él no tardará en defender la causa de ellos, para dar descanso al país y hacer temblar a los habitantes de Babilonia.
35 “Akwai takobi a kan Babiloniyawa!” In ji Ubangiji “a kan waɗanda suke zama a Babilon da kuma a kan fadawanta da masu hikimarta!
¡Espada contra los caldeos, dice Yahvé, y contra los habitantes de Babilonia; contra sus príncipes y contra sus sabios!
36 Akwai takobi a kan annabawan ƙaryanta! Za su zama wawaye. Akwai takobi a kan jarumawanta! Za su cika da tsoro.
¡Espada contra los impostores y se volverán estúpidos, espada contra sus combatientes y se amedrentarán!
37 Akwai takobi a kan dawakanta da kekunan yaƙinta da kuma dukan baƙin da suke cikin mayaƙanta! Za su zama mata. Akwai takobi a kan dukiyarta! Za a washe su.
¡Espada contra sus caballos y contra sus carros, contra toda la turba de gentes en medio de ella, y serán como mujeres! ¡Espada contra sus tesoros, que serán saqueados!
38 Fări a kan ruwanta! Za su bushe ƙaf. Gama ƙasa ce ta gumaka, gumakan da za su haukace da tsoro.
¡Sequedad sobre sus aguas, que se secarán! Porque es un país de ídolos, se vuelven locos con sus imágenes.
39 “Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can, a can kuma mujiya za tă zauna. Ba za a ƙara zauna ko a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara.
Por eso habitarán (allí) las fieras con los chacales; y los avestruces tendrán en ella su morada; nunca jamás será habitada, ni volverá a ser poblada en los siglos.
40 Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.
Como cuando Dios destruyó a Sodoma y Gomorra y las ciudades vecinas, dice Yahvé, no habitará hombre allí, ni morará en ella hijo de hombre.
41 “Duba! Ga sojoji suna zuwa daga arewa; babbar al’umma da sarakuna masu yawa suna tahowa daga iyakokin duniya.
He aquí que viene del Norte un pueblo; una nación grande y reyes poderosos; se alzan desde los extremos del orbe,
42 Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne marasa tausayi. Amonsu ya yi kamar rurin teku yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Babilon.
empuñan el arco y el venablo, son crueles y sin piedad, sus voces son como el mar que brama, montan caballos y vienen armados como guerreros contra ti, oh hija de Babilonia.
43 Sarkin Babilon ya ji rahotanni game da su, hannunsa kuma ya yi laƙwas. Wahala ta kama shi, zafi kamar na mace mai naƙuda.
El rey de Babel oye la noticia, y se le debilitan los brazos; le sobrevienen angustias y dolores como de parturienta.
44 Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai dausayi, zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan? Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni? Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?”
He aquí que sube como león de los boscajes del Jordán a los pastos de perenne verdor. Pero lo expulsaré de allí en un momento, y estableceré sobre él a quien Yo escogiere. Porque ¿quién hay como Yo, y quién me pedirá cuenta? ¿O quién es el pastor que pueda enfrentarse conmigo?”
45 Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Babilon, abin da ya nufa gāba da ƙasar Babiloniyawa. Za a kwashe ƙananan garkensu a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.
Por eso, oíd el designio que Yahvé ha tomado contra Babel, y los planes que ha trazado contra el país de los caldeos. Serán arrastrados hasta los endebles del rebaño y será devastado el pastizal juntamente con ellos.
46 Da jin an ci Babilon da yaƙi sai duniya ta girgiza; za a ji kukanta cikin al’ummai.
A la noticia de la conquista de Babilonia, temblará la tierra, darán alaridos las naciones.

< Irmiya 50 >