< Irmiya 48 >

1 Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.
論摩押。萬軍之耶和華-以色列的上帝如此說: 尼波有禍了!因變為荒場。 基列亭蒙羞被攻取; 米斯迦蒙羞被毀壞;
2 Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki.
摩押不再被稱讚。 有人在希實本設計謀害她,說: 來吧!我們將她剪除,不再成國。 瑪得緬哪,你也必默默無聲; 刀劍必追趕你。
3 Saurari kuka daga Horonayim, kukan risɓewa mai girma da hallaka.
從何羅念有喊荒涼大毀滅的哀聲:
4 Za a karye Mowab; ƙanananta za su yi kuka.
摩押毀滅了! 她的孩童發哀聲,使人聽見。
5 Sun haura hanyar zuwa Luhit, suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya; a hanyar da ta gangara zuwa Horonayim suna kuka a kan hallakar da aka ji.
人上魯希坡隨走隨哭, 因為在何羅念的下坡聽見毀滅的哀聲。
6 Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku; ku zama kamar kurmi a hamada.
你們要奔逃,自救性命, 獨自居住,好像曠野的杜松。
7 Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa.
你因倚靠自己所做的和自己的財寶必被攻取。 基抹和屬他的祭司、首領也要一同被擄去。
8 Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari, kuma ba wani garin da zai kuɓuta. Kwari zai lalace tudu kuma ya hallaka, domin Ubangiji ya faɗa.
行毀滅的必來到各城, 並無一城得免。 山谷必致敗落, 平原必被毀壞; 正如耶和華所說的。
9 Ku sa gishiri a kan Mowab, gama za tă zama kango; garuruwanta za su zama kufai, ba mazauna a cikinsu.
要將翅膀給摩押, 使她可以飛去。 她的城邑必致荒涼, 無人居住。 (
10 “La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji! La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini!
懶惰為耶和華行事的,必受咒詛;禁止刀劍不經血的,必受咒詛。)
11 “Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta, kamar ruwan inabin da aka bari lis, ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba ba tă tafi bauta ba. Saboda haka tana da ɗanɗanonta, kuma ƙanshinta bai canja ba.
摩押自幼年以來常享安逸, 如酒在渣滓上澄清, 沒有從這器皿倒在那器皿裏, 也未曾被擄去。 因此,它的原味尚存, 香氣未變。
12 Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna, su kuma zubar da ita waje. Za su bar tulunan ba kome a ciki su kuma farfashe tulunanta.
耶和華說:「日子將到,我必打發倒酒的往她那裏去,將她倒出來,倒空她的器皿,打碎她的罈子。
13 Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh, yadda gidan Isra’ila ya ji kunya sa’ad da suka dogara ga Betel.
摩押必因基抹羞愧,像以色列家從前倚靠伯特利的神羞愧一樣。
14 “Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’
你們怎麼說: 我們是勇士,是有勇力打仗的呢?
15 Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.
摩押變為荒場, 敵人上去進了她的城邑。 她所特選的少年人下去遭了殺戮; 這是君王-名為萬軍之耶和華說的。
16 “Fāɗuwar Mowab ta yi kusa; bala’inta zai auku nan da nan.
摩押的災殃臨近; 她的苦難速速來到。
17 Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’
凡在她四圍的和認識她名的, 你們都要為她悲傷,說: 那結實的杖和那美好的棍, 何竟折斷了呢?
18 “Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.
住在底本的民哪, 要從你榮耀的位上下來, 坐受乾渴; 因毀滅摩押的上來攻擊你, 毀壞了你的保障。
19 Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’
住亞羅珥的啊, 要站在道旁觀望, 問逃避的男人和逃脫的女人說: 是甚麼事呢?
20 An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab.
摩押因毀壞蒙羞; 你們要哀號呼喊, 要在亞嫩旁報告說: 摩押變為荒場!
21 Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,
「刑罰臨到平原之地的何倫、雅雜、米法押、
22 zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,
底本、尼波、伯‧低比拉太音、
23 zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,
基列亭、伯‧迦末、伯‧米恩、
24 zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.
加略、波斯拉,和摩押地遠近所有的城邑。
25 An karye ƙahon Mowab; an karye hannunta,” in ji Ubangiji.
摩押的角砍斷了,摩押的膀臂折斷了。這是耶和華說的。」
26 “Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya.
「你們要使摩押沉醉,因她向耶和華誇大。她要在自己所吐之中打滾,又要被人嗤笑。
27 Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba? Ba a kama shi cikin ɓarayi, har kaɗa kai na ba’a kike yi a duka sa’ad da kike magana game da shi?
摩押啊,你不曾嗤笑以色列嗎?她豈是在賊中查出來的呢?你每逢提到她便搖頭。
28 Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu, ku da kuke zama a Mowab. Ku zama kamar kurciyar da take sheƙarta a bakin kogo.
摩押的居民哪, 要離開城邑,住在山崖裏, 像鴿子在深淵口上搭窩。
29 “Mun ji labarin girman kan Mowab mun ji alfarma girmankanta da kumburinta girmankanta da fariyarta da renin zuciyarta.
我們聽說摩押人驕傲, 是極其驕傲; 聽說他自高自傲, 並且狂妄,居心自大。
30 Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji, “kuma taƙamarta ba ya cimma kome.
耶和華說: 我知道他的忿怒是虛空的; 他誇大的話一無所成。
31 Saboda haka zan yi kuka a kan Mowab gama dukan Mowab zan yi kuka, Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset.
因此,我要為摩押哀號, 為摩押全地呼喊; 人必為吉珥‧哈列設人歎息。
32 Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.
西比瑪的葡萄樹啊,我為你哀哭, 甚於雅謝人哀哭。 你的枝子蔓延過海, 直長到雅謝海。 那行毀滅的已經臨到你夏天的果子 和你所摘的葡萄。
33 Farin ciki da murna su ɓace daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab. Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi; ba wanda zai matse su da ihun farin ciki. Ko da yake akwai sowa sowar ba ta farin ciki ba ce.
肥田和摩押地的歡喜快樂都被奪去; 我使酒醡的酒絕流, 無人踹酒歡呼; 那歡呼卻變為仇敵的吶喊。
34 “Muryar kukansu na tashi daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz, daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya, gama har ruwan Nimrim ma sun bushe.
「希實本人發的哀聲達到以利亞利,直達到雅雜;從瑣珥達到何羅念,直到伊基拉‧施利施亞,因為寧林的水必然乾涸。」
35 A Mowab zan kawo ƙarshen waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu suna kuma ƙone turare ga allolinsu,” in ji Ubangiji.
耶和華說:「我必在摩押地使那在邱壇獻祭的,和那向他的神燒香的都斷絕了。
36 “Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa; tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset. Arzikin da suka samu ta ƙare.
我心腹為摩押哀鳴如簫,我心腸為吉珥‧哈列設人也是如此,因摩押人所得的財物都滅沒了。
37 An aske kowane kai aka kuma yanke kowane gemu aka kuma sa wa kowane kwankwaso rigar makoki.
「各人頭上光禿,鬍鬚剪短,手有劃傷,腰束麻布。
38 A kan dukan rufi a Mowab da kuma a dandalin jama’a babu wani abu sai kuka gama na karye Mowab kamar tulun da babu mai so,” in ji Ubangiji.
在摩押的各房頂上和街市上處處有人哀哭;因我打碎摩押,好像打碎無人喜悅的器皿。這是耶和華說的。
39 “Duba yadda aka ragargazar ta ita! Duba yadda suke kuka! Duba yadda Mowab ta juya bayanta da kunya! Mowab ta zama abin ba’a abin tsoro ga dukan waɗanda suke kewaye da ita.”
摩押何等毀壞!何等哀號!何等羞愧轉背!這樣,摩押必令四圍的人嗤笑驚駭。」
40 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa, tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab.
耶和華如此說: 仇敵必如大鷹飛起, 展開翅膀,攻擊摩押。
41 Za a ci Keriyot a kuma kame kagarai. A wannan rana zukatan jarumawan Mowab za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.
加略被攻取,保障也被佔據。 到那日,摩押的勇士心中疼痛如臨產的婦人。
42 Za a hallakar da Mowab a matsayin al’umma domin ta tayar wa Ubangiji.
摩押必被毀滅,不再成國, 因她向耶和華誇大。
43 Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen Mowab,” in ji Ubangiji.
耶和華說:摩押的居民哪, 恐懼、陷坑、網羅都臨近你。
44 “Duk wanda ya gudu daga razana zai fāɗa cikin rami, duk wanda ya haura daga rami zai fāɗa cikin tarko; gama zan kawo wa Mowab shekarar hukuncinta,” in ji Ubangiji.
躲避恐懼的必墜入陷坑; 從陷坑上來的必被網羅纏住; 因我必使追討之年臨到摩押。 這是耶和華說的。
45 “A ƙarƙashin Heshbon masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako, gama wuta ta mutu daga Heshbon, harshen wuta daga tsakiyar Sihon; ta ƙone goshin Mowab, ƙoƙon kai na’yan tayarwa masu surutu.
躲避的人無力站在希實本的影下; 因為有火從希實本發出, 有火焰出於西宏的城, 燒盡摩押的角和鬨嚷人的頭頂。
46 Kaitonki, ya Mowab! Mutanen Kemosh sun hallaka; an kai’ya’yanki maza daurin talala’ya’yanki mata zaman bauta.
摩押啊,你有禍了! 屬基抹的民滅亡了! 因你的眾子都被擄去, 你的眾女也被擄去。
47 “Duk da haka zan maido da wadatar Mowab a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. A nan hukuncin Mowab ya ƙare.
耶和華說: 到末後,我還要使被擄的摩押人歸回。 摩押受審判的話到此為止。

< Irmiya 48 >