< Irmiya 47 >
1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.
法老攻击迦萨之先,有耶和华论非利士人的话临到先知耶利米。
2 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa
耶和华如此说: 有水从北方发起,成为涨溢的河, 要涨过遍地和其中所有的, 并城和其中所住的。 人必呼喊; 境内的居民都必哀号。
3 da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas.
听见敌人壮马蹄跳的响声 和战车隆隆、车轮轰轰; 为父的手就发软, 不回头看顾儿女。
4 Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor.
因为日子将到, 要毁灭一切非利士人, 剪除帮助泰尔、西顿所剩下的人。 原来耶和华必毁灭非利士人, 就是迦斐托海岛余剩的人。
5 Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku?
迦萨成了光秃; 平原中所剩的亚实基伦归于无有。 你用刀划身,要到几时呢?
6 “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’
耶和华的刀剑哪,你到几时才止息呢? 你要入鞘,安靖不动。
7 Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”
耶和华既吩咐你攻击亚实基伦和海边之地, 他已经派定你,焉能止息呢?