< Irmiya 43 >
1 Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa mutane dukan maganar Ubangiji Allahnsu, duk abin da Ubangiji ya aike shi ya faɗa musu,
2 Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’
3 Amma Baruk ɗan Neriya yana zuga ka a kanmu don ka ba da mu ga Babiloniyawa, don su kashe mu ko su kai mu zaman bauta a Babilon.”
4 Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda.
5 A maimako, Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe raguwar Yahuda waɗanda suka dawo su zauna a ƙasar Yahuda daga dukan al’umman inda aka kora su.
6 Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.
7 Saboda haka suka shiga Masar cikin rashin biyayya ga Ubangiji suka tafi har can Tafanes.
8 A Tafanes maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
9 “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes.
10 Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu.
11 Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi.
12 Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi.
13 A can cikin haikalin rana a Masar zai rushe al’amudan duwatsu yă kuma ƙone haikalan allolin Masar.’”